Gwamnatin Tarayya ta amince kirkiro sabbin jami’o’i masu zaman kansu 20 a fadin kasar nan.
Cikin wadanda gwamnati ta amince da su sun hada da jami’ar Maryam Abacha dake Kano da kuma Jami’ar Nok dake Kaduna.
Tara daga cikin jami’o’in suna yankin Arewa Ta Tsakiya ne, Uku a yankin Kudu Masu Kusu, Biyu a Kudu Maso Gabas, Daya a Kudu Maso yamma sannan Biyar a Arewa Maso Yamma
Ga sunayen Jami’o’in
Topfaith University, Mkpatak, Akwa Ibom State; Thomas Adewumi University, Oko-Irese, Kwara State; Maranathan University, Mgbidi, Imo State; Ave Maria University, Piyanko, Nasarawa State, and Al-Istiqama University, Sumaila, Kano State.
Sauran sun hada da Mudiame University, Irrua, Edo State; Havilla University, Nde-Ikom, Cross River State; Claretian University of Nigeria, Nekede, Imo State; NOK University, Kachia, Kaduna State and Karl-Kumm University, Vom, Plateau.
Sannan kuma akwai James Hope University, Lagos, Lagos State; Maryam Abacha American University of Nigeria, Kano, Kano State; Capital City University, Kano, Kano State; Ahman Pategi University, Pategi, Kwara State, and the University of Offa, Offa, Kwara State.
Others are Mewar University, Masaka, Nasarawa State, Edusoko University, Bida, Niger State; Philomath University, Kuje, Abuja; Khadija University, Majia, Jigawa State and Anan University, Kwall, Plateau State.
Za a ba Jami’o’in lasisin soma aiki na shekaru 3 ana duba yanayin aikin su kafin a sabonta musu lasisin su.
Discussion about this post