Sojojin Najeriya sun yi ragaraga da gonar Shekau a Sambisa, sun rabawa wa mutanen gari ganima

0

Sojojin Najeriya sun darkaki gonar shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau inda suka yi ka kaca-kaca da gonar da ke cikin dajin Sambisa, suka gayyaci mazauna kauyukan dake kewaye da gonar su garzayo su kwashi ganima.

Sojojin kasa tare da hadin guiwar dakarun sama sun rika yi wa gonar luguden wuta tun daga garin Dikwa har suka isa wannan gona.

Bayan haka an rika jin wasu daga cikin Sojojin Najeriya na cewa, ” Wai ina Shekau ɗin ne, Ya fito mana in ba tsoro ba.

Daga nan sai mazauna kauyukan dake zagaye da gonar suka fantsama cikin ginar suka rika jidar ganimar abinci a buhuna suna kai wa gida.

Wannan harin nasara da sojojin Najeriya suka samu na daga cikin nasarorin da suka ta aamu a ƴan kwanakin nan, inda suke murkushe Boko Haram a garuwan Barno.

Share.

game da Author