Sojojin Najeriya su kadai ba za su iya magance Boko Haram ba, “tunda ba su ba ne su ka fara wannan rikicin ba.” Haka tsohon Hafsan Askarawan Najeriya, Janar Buratai mai ritaya ya bayyana a wurin da Kwamitin Majalisar Dattawa masu tantance sabbin jakadun kasashe da Shugaba Muhammadu Buhari ya nada kwanan nan.
A wurin tantancewar dai akwai sauran hafsoshin tsaro, wadanda Buhari ya sauke tare da Buratai, kuma duk sun sha ruwan tambayoyi daya bayan daya.
Dukkan su daya bayan daya an rika sheka masu ruwan tambayoyin da suka hada da irin nasarorin da su ka samu a lokacin aikin su da kuma irin abin da za su tinkara a yanzu idan sun zama jakadun Najeriya a kasashe daban-daban.
Buratai wanda shi ne mutum na biyu da aka yi wa tambayoyi, ya nuna takaicin yada rashin zaman lafiya ya barke musamman a Arewa masu Gabas.
A kan haka ya ce sojoji kadai ba za su iya dakile ta’addanci a kasar nan ba, musamman sai fa idan gwamnatin tarayya za ta rika samar da ababen more rayuwa a yankunan al’ummar da abin ya shafa.
“Saboda masu ta’addancin nan sun samu goyon baya da daurin gindin al’ummar yankunan da su ke a ciki.
“Aikin sojoji a kokarin dakile ta’addanci bangare daya ne kawai. Akwai sauran bangarorin da dole sai an gabatar wa jama’a ababen inganta rayuwa da sa hannu a fannonin tattalin arzikin su tun da farko.
“Ya kamata a samar da titina ko’ina. A samar da ci gaba a yankunan karkara ko’ina. Kamata ya yi a ce akwai makarantu da asibitoci da ayyukan yi a lungunan karkara.”
“Kananan Hukumomi da yawa a Arewa babu hanyoyi. Don haka shi ya sa a irin wadannan wurare ta’addanci da hare-hare ke kamari. Idan ba a magance irin wannan ba, to haka za a ci gaba da tafiya.’’
Discussion about this post