‘Shugaban Kasa na gobe’, haka dubban magoya bayan Okorocha suka rika cewa a Owerri

0

Dubban magoya bayan tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha sun yi dafifi a manyan titunan garin Owerri, babban birnin jihar Imo, suna yi masa lale marhaban da zuwa jihar.

Cikin jawabin da shugaban matasan bangaren APCn Okorocha, Kenneth Emelu, yayi ya bayyana cewa basu da uba ba su da uwa a Najeriya da ya wuce Okorocha, shugaban Najeriya na gobe.

” Muna tare da kai a ko da yaushe domin a faɗin yankin kudu babu wanda ya fika sanuwa da jajircewa. Ga ka haziki kuma fitaccen ɗan siyasa. Wani abu da kake dashi da basu da shi shine rungume kowa naka, kai kasai gayya.

” A dalilin haka ya sa muke tare da kai kuma muke yi maka fatan alkhairi a kullum.

Share.

game da Author