Shirin Kula Da Dattawa Na Kasa ya samu karbuwa a hannun Gwamnatin Tarayya – Minista Sadiya

0

An bada tabbatacin cewa Shirin Kula da Dattawa na Kasa ya samu amincewar Majalisar Gudanarwa ta Tarayya (FEC).

Shirin wanda na Kula Da Masu Manyan Shekaru ta Ƙasa, a turance ‘National Policy on Aging’, a matsayin wani bangare ne na ƙoƙarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na tabbatar da tsaron lafiya da tattalin arzikin mutanen da yawan shekaru ya cim masu.

Ministar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouk, ita ce ta bayyana haka ga manema labarai a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Laraba, jim kadan bayan taron hukumar, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

A cewar ta, manufar shirin ita ce domin a tabbatar da cewa dattijai sun samu kariya, tsaro, damar shiga a dama da su da kuma cikakkiyar kula tare da samun cikar buri da gamsuwa.

Ta ce, “Shirin ya hado dimbin al’amura da damarmaki saboda dattawa, da dattawa masu wata nakasa, da dattawa ‘yan gudun hijira, da dattawa da ke noma a yankunan birane da karkara a Najeriya.”

A wani labarin kuma, a kwanan baya ne Sadiya Farouq ta nemi a rika kula da nakasassun Najeriya kamar yadda ake yi a wasu kasashe, inda ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa da nakasassun da ke Najeriya jeriya hanyoyin da za su rika bi a dukkan gine-gine da wurare na gwamnati irin su filayen jirgin sama, tashoshin jirgin kasa da na mota da makarantu.

Ministar ta yi kiran ne a lokacin da ta gabatar da Shugaba da membobi da Babban Sakataren Cibiyar Nakasassu ta Kasa ga Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Sadiya ta gode wa Shugaban Kasa saboda yadda ya amsa kiran nakasassun ta hanyar rattaba hannu kan Dokar Kula da Nakasassu ta Kasa sannan ya kafa Hukumar NaKasassu ta Kasa. Amma ta yi nuni da cewa mutane masu nakasa a kasar nan an ware su daga cin moriyar wasu ababe na more rayuwa.

Ta ce sama da kashi 95 cikin dari na gine-ginen gwamnati da ke kasar nan ba su shiguwa a wajen nakasassu sannan yawancin su su na bukatar wasu na’urori da hanyoyin kimiyya da fasaha da za su taimake su wajen samun ilimi da koyo a cikin sauki.

Share.

game da Author