Shirin ajiya don yin aikin Hajji zai bunkasa harkar kasuwanci kanana da manya, tanadi da saka jari

0

Sabon Shirin Ajiya don yin Aikin Hajji da Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) tare da hadin gwiwar Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai na Jiha da Bankin Jaiz zai bunkasa hada-hadar kudade a kasar nan.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da shirin wayar da kan mutane game da shirin a garin Dutse, Jihar Jigawa, gwamna Abubakar Badaru ya ce shirin zai taimaka wa mutane musamman a yankunan karkara su rungumi yin tanadi don saka jari a nan gaba koda bayan kammala aikin Hajji.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Umar Namadi, ya ce gwamnatin jihar za ta hada kai da hukumar alhazai domin wayar da kan mutanen jibar musamman mazauna karkara dake kananan hukumomin jihar.

Haka shima Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce wannan shirin zai kawo sauki ga musulmin da ke son zuwa aikin Hajji kuma lallai akwai tabbacin hakan zai inganta tsarin zuwa aikin Hajji a duniya.

Gwamnan, wanda Babban Sakatare a gwamnatin jibar ya wakilta. George Egberasie ya ƙaddamar da shirin a Benin inda ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa za ta goyi bayan shirin saboda shirine da zai haɓaka tattalin arzikin masu ajiya da kuma na mutane baki daya.

Mataimakin gwamnan jihar Katsina, Mannir Yakubu, wanda Babban Sakatare a ofishin gwamnan, Abubakar Aliyu ya wakilta, ya yaba wa duk masu ruwa da tsaki a cikin shirin kuma ya yi alkawarin goyon bayan gwamnati don samun nasarar.

Ya ce, “Tsarin ana tafiyar da shi ne ta fuskar tattalin arziki kasancewarsa na wani hanyar saka jari.

Ya shawarci cewa bai kamata a hanzarta shirin ba don samun nasarar da ake nema. Ya kuma yi gargaɗi game da masu zamba wato wadanda za su iya yin amfani da damar wajen yi wa mutane zamba.

Da yake jawabi, Manajan Daraktan Bankin Jaiz, Hassan Usman ya ce Bankin zai tabbatar da kyakkyawan tsarin kula da kudaden daga shirin ta hanyar sanya shi a cikin hada-hadar kasuwanci da ya zai bi tsarin Shariah.

A jawabin da yayi a lokacin taron, Shugaban Hukumar NAHCON, Zikirullah Kunle Hassan, ya bayyana cewa HSS shiri ne da za a gudanar yadda tsarin zai kasance wandanda suka zo da farko da su za a fara.

Share.

game da Author