Kungiyar Taratsin Kafa Biafra (IPOB), sun gwamnati Najeriya ta dakatar da sojojin sama da ke yi wa wasu kauyukan yankin shawagi cewa yin haka tsakalar su ne su fito yaki.
Kungiyar ta ce manyan jiragen sojojin sama na yi wa garin Orlu dake jihar Imo shawagi da ba su san menene dalilin yin haka ba.
Kungiyar ta ce sojojin Najeriya sun wuce gona da iri, saboda haka suma za su to domin kare martaba da muatanen yankin su.
Kakakin ‘yan sandan jihar Imo ya ce bashi da masaniyar ko akwai wani hari da Sojojin sama suka kai wa wata al’umma a jihar Imo. Sai dai kuma wani mai suna Chika Edoziem ya ce babu gudu ba ja da baya, a shirye IPOB ta ke ta maida martani idan aka cika yi wa mutanen ta wato inyamirai barazana.