Sau hudu ana siyar da ni ga masu safarar mutani – Wani matashi

0

Wani matashi da ya dawo daga kasar Libiya mai suna Terry Ikponmwosa ya bayyana cewa sau biyar ana siyar da shi ga masu safarar mutane ana cefanensa tsakanin Najeriya da kasashen turai da Wasu kasashen Afrika.

Ikponmwosa mai shekaru 31 ya ce ya fada hannun wadannan mutane a loka in da ya nemi ficewa daga Najeria zuwa kasar Libya.

“Da na gama makarantar sankandare sai na fara sana’ar siyar da siminti.

“Ina samun kudi a wannan sana’a da nake yi amma sai na ga Ina bukatan zama hamshakin mai kudi.

“Wani abokina ya bani labarin yadda idan mutum ya shiga kasar Turai ta kasar Libiya yana zama mai kudi. A dalilin haka na kwaso duk kudade na Naira miliyan 1 na danka wa wani mutum da zai taimaka min wajen kaini kasar Turai.

“Shago na kuma na ba wani abokina ya ci gaba da sana’ar yana ba ‘yan uwana kudin cinikin da ya yi. Abokina ya siyar da shagon ya gudu da kudin.

“Ba tare da sani naba mutumin da zai taimaka mun zuwa kasar Turai ya siyar da ni wajen wani a Agbor jihar Delta da suna cewa zai hada ni da wani da zai taimaka mun.

Ikponmwosa ya ce turawa sun kama su suka daure su a kurkuku a lokacin da suke kokarin shiga kasar.

Share.

game da Author