Sanatoci da ‘Yan Majalisar Zamfara na so Buhari ya yi wa tubabbun ‘yan bindiga afuwa

0

A ranar da ‘yan bindiga su ka yi awon-gaba da dalibai 42 daga Makarantar Sakandaren Kimiyya ta Kagara a Jihar Neja, su kuma ‘yan majalisar Zamfara kira su ka yi ga Shugaba Muhammadu Buhari ya i wa tubabbun ‘yan bindiga afuwa.

PREMIUM TIMES ta buga labarin garkuwar da aka yi da daliban, malaman makaranta da wasu ’ya’yan malaman makarantar.

Jim kadan bayan yin awon gaba da daliban, sai kuma a gefe daya wasu ‘yan majalisa daga jihar Zamfara su ka yi kira ga Shugaba Buhari ya yi wa tubabbun ’yan bindiga afuwa.

‘Yan Majalisar na Tarayya daga Jihar Zamfara, sun yi wannan kira ne ga Buhari a ranar Laraba.

Sun ce idan Buhari a Gwamnatin Tarayya ta yi masu afuwa, to hakan zai sa su ajiye makaman su, su damka wa gwamnati makaman.

A na ta bangaren sun ce ita kuma gwamnati sai ta saka masu da godiya, ba su ’yan kudaden sakawa aljihu da kuma koya masu sana’o’in dogaro da kai sannan kuma a ilmantar da sub akin gwargwado.

Sun dai bada misali da irin afuwar da tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Yar’Adua ya yi wa tsagerun Neja-Delta.

Kafin afuwar da Umaru ya yi wa tsagerun Neja-Delta cikin 2009, yankin ya kasance cikin hare-haren bututun mai ta yadda komai ya nemi tsayawa cak. Sannan kuma harkokin hako mai ya nemi gagara a Najeriya.

To irin wannan afuwar ce ake nema Buhari ya yi wa ’yan bindiga wadanda su ka fitini yankunan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, kamar yadda ‘yan majalisar Jihar Zamfara su ka nema.

Wadanda su ka a yi wannan afuwar sun hada da sanatocin su uku da kuma ‘yan majalisar tarayya hudu.

Jagoran neman afuwar shi ne Sanata Sabiu Ya’u daga Zamfara ta Arewa.

Ya bayyana cewa lokacin da Gwamna Matawalle ya hau mulki cikin 2019, ya gaji wani tsarin sulhu da ‘yan bindiga, wanda ya yi amfani da shi, kuma aka samu saukin lamarin sosai.

Ya kara da cewa tuni da dama wadanda su ka kaurace wa gidajen su da gonakin su, su na ta komawa gidajen na su.

Share.

game da Author