Sanata Uba Sani ya yi tir da harin Birnin Gwari da Kajuru

0

Sanatan dake wakiltar Kaduna Ta tsakiya a Majalisar Dattawa, Sanata Uba Sani ya yi tir da harin da ‘yan bindiga suka kai kauyukan Kananan hukumomin Birnin Gwari da Kajuru.

Sanatan ya bayyana rashin jin dadin sa bisa wannan hari yana mai mika ta’aziyyar sa ga ‘yan uwan wadanda aka rasa a wannan harin sannan kuma da jaddada kokarin gwamnati na ganin an kawo karshen hare-haren kauyuka a yankin wadanda basuji ba basu gani ba.

Bayan haka ya jinjina wa gwamnatin jihar Kaduna karkashin gwamna Nasir El-Rufai kan kokarin da take yi wajen ganin an kawo Karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.

Sanatan ya kara da cewa za a aika da kayan tallafi na gaggawa ga wadanda wannan ibtila’i ya afka wa yana mai kira ga mutane da su kwantar da hankulan su.

Sannan kuma ya mika godiyar sa ga mutanen yankin Kaduna ta tsakiya bisa zaman lafiya mutane ke yi a tsakanin su cewa ba zai yi kasa ba wajen ganin yankin Kaduna ta tsakiya ta amfana da duk cigaba da ban da ban da zai kawo musu a matsayin sa na wakilin su a majalisar Dattawa.

Zuwa yanzu Sanata Una Sani na ci gaba ayyukan ingata ilimi a makarantun gundumarsa inda ake gina wa kowacce sakandare dakin nazari da karatun Kofuta wato na’ura mai kwakwalwa.

Share.

game da Author