Sanata Adeyemi fa ‘dan iskan kauye’ ne kawai –Gwamnatin Abia

0

Gwamnatin jihar Abia ta kira Sanata Smart Adeyemi da cewa ‘dan iskan kauye ne kawai’, wanda ba shi da tarbiyya.

Gwamnatin ta ce ba don Adeyemi na da rigar kariya ta Majalisar Dattawa ba, to da gwamnatin ta Abia ta maka shi kotu, domin a wanke masa idanu daga giribtun kauyancin sa.

Kiran Adeyemi da wannan suna ya biyo bayan shi Adeyemi ya fassara Gwamnan Jihar Abia Ikpeazu cewa tantirin dan giya ne, kuma gwamnatin sa gwamnatin ‘yan giya ce kawai.

Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Abia, John Okiyi ya fitar ga manema labarai, ya bayyana Sanata Smart Adeyemi da cewa “dan iskan kauye ne, wanda duk a lokacin da ya buda bakin sa, to kalaman sa wawanci ne, sai kuma kara tabbatar da gidadancin sa.

A Je A Yi Gwaji A Gano Mashayin Giya Tsakanin Sanata Adeyemi da Gwamnan Abia –Kwamishina

“Ya kamata Adeyemi ya sani cewa Gwamna Okezie Ikpeazu ba ya daga kwalabe, ba ya shan kowace irin barasa. Kuma ina kalubalantar Sanata Adeyemi ya gayyaci gwamnan Abia su je wani kebantaccen wuri, duk a yi masu gwajin wanda ke da ruwan barasa a jikin sa a tsakanin su, domin a tantance dan giya.

“Kuma idan za a yi gwajin, to Sanata Adeyemi ya je shi da Gwamnan jihar san a Kogi, shi ma a yi masa gwajin, domina tantance wane gwamna ne dan giya, tsakanin na Abia da na Kogi.

“Wai in banda rashin kunya, mutum kamar Sanata Adeyemi, wanda ‘yan jarida ‘yan uwan sa su ka ce shi ne tantagaryar mutumin banzan da ya taba shugabantar Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa, shi ne wai zai kira mutum mai mutunci, Gwamnan Abia wai dan giya.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin raddin da Gwamnan Abia ta bakin kakakin yada labaran sa, ya maida wa Sanata Adeyemi cewa mahaukaci ne tuburan, bayan Adeyemi ya kira shi dan giya.

Gwamnan Jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya bayyana cewa Sanata Smart Adeyemi na Jihar Kogi tantagaryar mahaukaci ne, mai tabin hankalin da ya kamata a ce an gaggauta turawa gidan mahaukata.

Ya kara da cewa Adeyemi na fama da wata cuta, wadda kwakwalwar sa ta kwarkwance, har ya ke furta kalamai wadanda mai cikakkken hankali ba zai iya furtawa ba.

Yayin da Adeyemi ke bayani a zauren Majalisar Dattawa, ya ce Ikpeazu tantirin dan giya ne, kuma gwamnatin sa “gwamnatin ‘yan giya ce, masu sha su yi mankas.”

Adeyemi ya yi wannan kakkausan furucin a lokacin da ake mahawara kan Shirin Kiyaye Lafiyar Dalibai a Makarantu.

“A wasu sassan Najeeriya a yau, mu na da masahuran mutane masu kaifin kwakwalwa da basira da zurfin ilmi. Amma jihar kamar Abia, ‘yan giya ne ke mulkin ta, shi kuma gwamnan su ba shi da wani aiki sai shan barasa mai tsada, wato ‘champagne’.

“Al’ummar Abia ba su yi dacen gwamna ba. Al’ummar Abia sun shiga cikin tsomomuwar kuncin rayuwa.” Inji Sanata Adeyemi.

Yayin da PREMIUM TIMES ta tuntubi kakakin yada labarai na Gwamnan Jihar Abia, mai suna Onyebuchi Ememanka, sai ya fitar da takardar manema labarai, inda ya fassara Sanata Adeyemi da “mutum mai fama da ciwon hauka.”

Ya yi kiran jama’a su yi watsi da shirmen maganganun Adeyemi, wanda ya ce kwakwalwar sa ta tabu, bai fahimci batun ake tattaunawa a majalisa a lokacin da ya yi furucin na sa ba.

“Ku rabu da kwarkwantacce kawai. Kan sa da motsi shi ya sa bai ma san halin da ya ke ciki ba. Ya kamata ya san cewa Jihar Abia ta fi jihar Kogi komai na ci gaba. Kwanan nan fa Hukumar Kididdigar Alkaluman bayanai (NBS) lissafa Abia ta uku a jerin jihohin da masu zuba jari daga waje su ka sa wa albarkar jari. Legas da Abuja ne kadai a gaban Abia.

Daga nan sanarwar daga Gidan Gwamnatin Abia ta ci gaba da yi wa Adeyemi da Jihar Kogi inda ya fito kaca-kaca da gori.

Share.

game da Author