SACE DALIBAN JANGEBE: An rufe makarantun kwana 10 dake jihar Kano

0

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rufe makarantun kwana 10 dake fadin jihar.

Kwamishinan ilimin jihar Sanusi Kiru ya sanar da haka a na’urar daukan magana da aka aika wa manema labarai.

Kiru ya ce gwamnatin Kano ta dauki wannan mataki ne domin kare daliban dake makarantun kwana ‘ganin yadda yanzu suka zama kama kaji daga an bushi iska sai a garzaya a sace su’.

Sunayen makarantan da gwamnatin Kano ta rufe

Makarantar kwana na Ajingi, makarantar kwana na mata dake Sumaila, makarantar mata dake Jogana, makarantar mata dake Gezawa da makarantar mata dake Kafin Maiyaki, makarantar Maitama Sule dake Gaya, makarantar sakandaren na mata dake Kachako, makarantar mata dake Kunchi, makarantar dake Karaye, kwalejin koyar da Arabi na gwamnati dake Albasu.

Kiru ya yi kira ga iyaye su gaggauta zuwa makarantun da aka rufe su tafi da ‘ya’yan su.

Shima gwamnan Zamfara, Matawalle ya sanar da rufe makarantun jihar a dalilin sace yara da aka yi a Jangebe.

Gwamna Matawalle ya bayyana cewa tuni gwamnati ta aika da jami’an tsaro domin a ceto wadannan yaran makaranta.

“Za mu rika sanar da iyayen daliban halin da ake ciki.

Matawalle ya yi kira ga mutanen jihar gaba daya da su hada hannu da gwamnati da bata goyon baya don ganin an yi nasaran ceto daliban daga hannu mahara.

“Ina kira ga mutane da kada su yadda a hure musu kunne da shigo da siyasa cikin al’amarin da ya faru domin yin haka ba zai haifar musu da da mai Ido ba.

Share.

game da Author