Babban Mashawarci kan yaki da rashawa na Shugaban Kasa, Itse Sagay, ya bayyana cewa ya jin tsoron lallai Ministan Shari’a Abubakar Malami ba zai bar sabon Shugaban EFCC, Abdulrashid Bawa ya yi aiki ba tare da ya yi masa katsalandan ba.
Malami wanda ya fito jiha daya da Bawa, shi ne ya haddasa musabbabin korar da aka yi wa tsohon shugaban riko na EFCC, Ibrahim Magu.
Har yau kuma Minista Malami din ne dai ya yi ruwa da tsaki aka nada Abdulrashid Bawa, wanda su ka fito jiha daya.
Sagay, wanda shi ne Shugaban Kwamitin Mashawartan Shugaban Kasa a fannin cin hanci da rashawa, wato PACAC, ya bayyana a ranar Laraba cewa, a gaskiya bai gamsu da nadin da aka yi wa Bawa ba, saboda jiha daya ya fito da Ministan Shari’a, Abubakar Malami.
A cikin wata tattaunawa da jaridar PUNCH, Sagay ya ce akwai ma yiwuwar Bawa da Malami ‘yan uwan juna ne na kusa ko na nesa, tunda daga jiha daya su ka fito.
Sagay ya ce shi ya na magana ne bisa hujjojin da ya ke da su na katsalandan din da Malami ya rika yi wa EFCC a baya, ballantana kuma yanzu ga shi dan jihar sa ne aka nada. Sannan kuma da hannun Malami din wajen nada Bawa.
“Gaskiya bai kamata a ce Shugaban EFCC da kuma Ministan Shari’a duk su kasance sun fito daga jiha daya ba. Kuma zai iya kasancewa ma su na da kusanci na ‘yan uwantaka. Kenan Malami ba zai rika barin EFCC ta na gudanar da aikin kashin kan ta ba, ba tare da yi mata katsalandan ba.
“EFCC ba ‘yan siyasa ba ne. Amma shi Malami dan siyasa ne. Kuma ba zai rasa abokai da aminan masu lashi a gindi ba.
Sai dai kuma Malami ya bayyana cewa ba shi da dangantaka da Bawa, kuma ba Karamar Hukuma daya suka fito ba.
Malami dan Birnin Kebbi ne, shi kuma Bawa dan Jega ne.
Malami ya ce bai taba yin wata hulda da Bawa ba ta kusa ko ta nesa, duk kuwa da cewa a EFCC ya ke aiki.
Ya kara da cewa hazaka da kwazon Bawa da kuma kishin sa ne su ka sa ya cancanci zama sabon Shugaban Hukumar EFCC.