Tsohon gwamnan jihar Ogun kuma jigo a Jam’iyyar PDP Gbenga Daniel ya tattara nasa-inasa ya tsindima cikin jam’iyyar APC.
Daniel ya ce canja shekar da ya yi ya biyo bayan matsalar da PDP ta afka ciki ne na tangal-tangal da take yi da kuma yadda lissafin siyasar kasar nan yake canja salo.
“Ba wai ba za mu ci karo kalubale a cikin jam’iyyar da muka koma bane ko kuma su basu da nasu rigingimun amma wata tafi wata. Abun da muka yi yanzu shine ya fi dacewa mu yi domin ci gaban mu da yankin mu. Idan aka samu sauyi nan gaba zamu dauke shi yadda yazo. Ina mika gaisuwa ta ga kowa da kowa”.
Ana sa ran gwamnonin jihohin Ogun, Dapo Abiodun, Yobe, Mai Mala Buni; Kaduna, Nasir El-Rufai; Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu; da na Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar.
Bayan haka kuma daga majalisar Wakilai, ƴan majalisa biyu sun canja sheka saga jam’iyyun su zuwa jam’iyyar APC.
Wadanda suka koma APC din sun hada da Blessing Onuh (APGA-Benue) da Yakubu Abdullahi (PRP-Bauchi).
Idan ba a manta ba, duk a cikin ƴan kwanakin nan tsohon Sanata daga jihar Osun, Omisore shima ya canja sheƙa zuwa jami’iyyar APC.