Rufe kasuwancin hada-hadar kudin intanet ‘Cryptocurrency’ ya tada hankalin ‘yan Najeriya

0

Babban Bankin Najeriya CBN ya umarci bankunan Najeriya su rufe asusun ‘yan kasuwa da kamfanoni masu amfani da kudin yanar gizo wanda ake kira da(cryptocurrency).

CBN ya fitar da sanarwar haka ranar Juma’a inda ya umurci bankunan dake hadahadar kudi a fadin kasar nan da kuma wasu kamfanoni da ba na hadahadar kudi ba wato NBFI da duk kamfanin da ke hadahadar kudi a kasar nan su dakatar da wannan kasuwanci na kudin ‘yanar gizo wato kudin intanet.

Babban darektan dake kula da harkokin bankuna Bello Hassan da Darektan tsare-tsaren biyan kudade Musa Jimo ne suka saka hannu a wannan takarda.

Takardar ta ce ” Babban bankin Najeriya CBN yana tunatar da ma’aikatun da kamfanonin da ke mu’amala da kudaden intanet ko kuma dillalansu cewa yin haka haramun ne kowa yayi sallama da harkar.

“Saboda haka, an umarci dukkanin NBFIs da NBFIs da OFIs da su tantance mutanen da ke amfani da irin wadannan kudade sannan su rufe asusun ajiyarsu dake bankunan su nan take.

Idan ba a manta ba a shekarar 2017, Babban bankin kasa ya bayyana irin wadannan kudade na intanet Kamar su bitcoin wanda shine yafi suna da litecoin da sauran ire-iren wadannan kudade na intanet cewa ana amfani da su ne wurin kashe wa ‘yan ta’adda da kuma daukar nauyin ta’addanci da irin wadannan kudade.

Wani abu da yake a boye da wannan kasuwanci na kudin intanet shine ba a iya bin sawunsa saboda karkakakaf din sa a yanar gizo ake gudanar dashi kuma ba za ka ganshi a zahiri ba sai dai a asusunka na yanar gizo. Hakan yasa akan yi amfani da wadannan kudade wajen daukar nauyin ta’addanci.

‘Yan Najeriya da dama sun nana rashin jin dadin su kan wannan shawara da babban bankin Najeriya ya dauka da rufe wannan kasuwa a kasar nan.

Da yawa sun ce kasuwancin kudi na yanar gizo wato intanet yana taimakawa matasa da basu da aikin yi masu yawa a kasar nan.

Share.

game da Author