PSG ta yi wasan kura da Barcelona a ‘Champions League’

0

Kungiyar Kwallon kafa ta Barcelona ta sha kashi a hannu PSG ta kasar Faransa a wasan Champions league da aka buga ranar Talata.

Abu kamar wasa, karamar maga ta zama babba.

Barcelona ce ta fara jefa kwallo a ragar PSG ta hannu shahararren dan wasanta, Leo Messi. Sai dai kuma ashe ya ciyo mai ‘ya’ya ne.

Tun da Messi ya jefa wannan kwallo da sai kamar an saki kura ne a garkin tumaki, ‘yan wasan PSG suka rika wasan kura da Barcelona, ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba.

Da suka fara dura wa Barcelona Kwallo sai da suka jefa kwallaye har hudu a ragar su. Haka dai aka yi ta yi har Alkalin wasa ya hura tashi.

idan ba a manta ba, a kakakr wasan bara, Bayern Munich ta lallasa Barcelona da ci 8 da 2 a irin haka.

Share.

game da Author