Jam’iyyar PDP mai mulki ta shiga rudu bayan fitar wata takarda mai dauke da bayanan yadda aka yi binciken kudin jam’iyyar ta fito sarari.
A cikin takardar, an zargi shugabannin jam’iyya da yin rub-da-ciki a kan wasu makudan kudade adadin milyoyin nairori.
An fallasa takardar wadda jami’an binciken kudin jam’iyya su ka fitar, mai dauke da zargin yadda Shugabannin PDP a karkashin jagorancin Uche Secondus su ka yi almubazzaranci da bilyoyin nairorin jam’iyya, a cikin shekaru uku.
Babban Mai Binciken Kudi na PDP, Adamu Mustapha, ya bayyana cewa shugabannin jam’iyya sun hana bangaren sa gani ko mallaka ko sanin yadda aka kashe kudaden jam’iyyar PDP, tun daga shekarar 2017 har zuwa yau.
“A matsayi na Mai Binciken Kudin PDP, amma an hana ni ganin kwafe-kwafen bayanan yadda aka kashe kuaden jam’iyyar PDP.
“Na kasa sanin adadin kudaden da su ka rika shigowa, ranar da su ka rika shigowa da kuma yadda su ke fitar da kudaden da abin da aka rika yi da su.”
Daga nan sai Mustapha ya yi kira ga shugabannin jam’iyya su tara manema labarai su yi masu jawabin yadda aka kashe kudaden jam’iyyar PDP.
Sai dai kuma Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Ologbondiyan, ya maida radin cewa dukkan batutuwan da Mai Binciken Kudi ya yi magana a cikin rahoton sa, shugabanin jam’iyyar duk bayar da amsar su.
Sai dai kuma Mustapha ya ce babu wani batu da PDP ta bayar da amsa, domin a wurin yaron Kwamitin Zartaswa da na Gudanarwa duk ya sha tashi ya yi wannan tsokaci, amma ba a yi komai ba, domin bada amsar yadda wasu bilyoyin kudade su ka salwanta, a cikin shekaru uku.
Ya ce an rasa abin da aka yi da wata naira milyan 500 da aka cira daga kudin jam’iyya.
Sai kuma bilyoyin kudaden da su ka salwanta, wadanda aka tara daga kudaden sayen katin shaidar dan jam’iyya da na taron gangamin jam’iyya, wato ‘congress.’
“Daga ranar da aka rantsar da shugabannin yanzu zuwa yau, an rasa yadda aka yi da naira bilyan 10. Kuma an kasa yi mana bayani gamsasshe.” Inji Mustapha.