PDP ta gargadi Gwamnatin Buhari kada ta kara farashin fetur

0

Jam’iyyar PDP ta gargadi Gwamnatin Tarayya cewa kada fa kara jefa ’yan Najeriya cikin kuncin talaucin da ta rigaya ta jefa ta, wajen kokarin kara kudin litar fetur da ake rade-radin za a yi.

PDP ta yi wannan gargadin ne cikin wata sanarwa da kakain yada labarai na jam’iyyar, Kola Ologbondiyan ya fitar wa manema labarai a ranar Asabar, a Abuja.

Ologbondiyan ya ce tuni Gwamnatin APC ta jefa kasar nan cikin halin kuncin da ake fama da fatara da talauci da rashin zaman lafiya.

Don haka a cewar PDP, karin kudin fetur din da aka yi cikin watan Nuwamba, 2020 zuwa lita daya naira 170, ya jefa mutane cikin kunci. Sake yin wani karin kuma zai gigita jama’a inji PDP.

Daga nan sai Ologbondiyan ya ce idan aka yi wani karin, to zai karasa rafke ‘yan Najeriya su zube kasa, saboda halin kaka-ni-ka-yi.

“Karin kudin fetur zai kara jefa talakawa sama da milyan 90 cikin wani mawuyacin halin da ya fi na talaucin da su ke fama da shina yanzu. Domin sai farashin abinci da sufuri da komai ya karu. Musamman idan aka yi la’akari da cewa mutum milyan 90 din nan, babu ami iya samun naira 500 ta kan sa a kowace rana.”

Ya ce abin haushi ne har da mahukuntan Najeriya ke kwatanta farashin litar mai a wasu kasashe da Najeriya.

“Mafi karanci albashi fa naira 30,000 a wata, wato naira 1,000 a kullum. To ya za ka hada da mafi karancin albashin Saudi Araba na Riyal 3,000. Ka ga idan ka auna Riyal da Naira, to kowane mai karamin albashi a Saudi ya na karbar naira 10,161 a kowace rana kenan.”

“A kan haka jam’iyyar mu na shaida wa gwamnatin tarayya da ’yan Najeriya cewa ba ta goyon baya, kuma ba za ta goyi bayan karin kudin fetur a wannan yanayi da jama’a ke ciki ba, wanda abinci da zaman lafiya ya gagare su.”

Share.

game da Author