Gwamnan Zamfara Bello Matwalle ya jaddada cewa babu abin da yafi gwamnoni su runguma wajen kawo karshen hare-hen ‘yan bindiga da garkuwa da mutane da wuce sulhu.
” Sulhu ne yafi dacewa dukkanmu mu runguma domin babu abinda sulhu baya iya kawo. Mu zauna a teburi daya a tattauna da mahara a yi sulhu sai a samu zaman lafiya kuma wannan shine na yarda.
Matawalle ya kara da cewa ba wai don za ayi sulhu shi kenan ba za a kuma yaki wadanda suka ki a yi sulhu da su ba. ” yin sulhun dai shine ya fi dace gwamnoni su runguma idan har ana so a kawo harshen wannan matsala.
Matawalle ya fadi haka ne a wajen kaddamar da aikin titi a jihar Adamawa ranar Laraba.
PREMIUM TIMES ta buga labarin matsayar gwamnan Kaduna game da ‘yan bindiga inda ya ce shi bai yarda da maganar ayi sulhu da su ba.
” Ni ban ga dalilin yin sulhu da dan bindiga ba, mutumin da ya saba ya na zaune a kawo masa miliyoyin naira a inda yake lokacin da yake so, ba zai yarda ko kuma ya hakura wai ya koma cikin halin da yake a baya ba sai yaga uwar bari.
” Abinda ya kama ta mu yi shine mu hada kai dukkan mu mu garzaya Abuja a bamu sojoji da zakakuman jami’an tsaro gaba daya a tura su cikin dazukan nan su yi wa mutanen nan farad daya. Shine maganin wannan matsala da ya addabe mu ba yin sulhu da dan ta’adda ba.