NEJA: An kusa sako daliban da aka yi garkuwa da su – Gwamnan Neja

0

Gwamnan Jihar Neja Abubakar Bello ya bayyana cewa tattaunawar sako daliban sakandaren Kagara da malamai uku da kuma iyalai 17 da masu garkuwa su ka kama a Kagara, cikin Karamar Hukumar Rafi.

Bello yace gwamnati na yin duk abinda ya dace domin ganin an sako dabiban da sauran mutanen da aka kama su tare.

Ya ce gwamnatin jihar Neja na korarin ganin an sako su tare da tuntubar Gwamnatin Tarayya kan duk wani taku ko matsaya da aka cimma.

“Zuwa yanzu dai babu wani karin bayani tukunna, baya ga wanda mu ke da shi kuma mun bayyana maku. Babban abin da ke gaban mu shi ne a karbo su su dawo gida cikin koshin lafiya. Ana yawa wadansu ji-ta-ji-ta, amma dai ba za mu tsaya kula wannan batun ba tukunna.”

Ya ce jihar Neja na amfani da matakai biyu wajen ganin an sako daliban da sauran wadanda aka kama din.

Sannan kuma ya tabbatar wa iyayen yara da sauran iyalai cewa su yi hakuri an kusa dawo da dangin na su a gida.

Ya fayyace yadda shahararren malami Sheikh Ahmed Gumi ya amince zai taimaka wa gwamnatin jihar Neja. Kuma an tura wa gwamnan cikakken bayanin abubuwan da Gumi din ya gano a ganawar sa da masu garkuwa da mutane.

Daga nan ya yi roko ga sarakunan gargajiya su taimaka wa jami’an tsaro wajen tona asirin duk wata mabuyar masu aikata muggan laifuka.

Dangane da lalacewar da sakandaren Kagara ta yi kuwa, Bello ya ce tuni aka lissafa da ita cikin wani gagarimin garambawul da jihar za ta yi wa fannin ilmi da makarantu baki daya a jihar.

Shi ma Gumi ya shaida wa manema labarai cewa ana samun daidaiton sulhuntawa a sako daliban da sauran mutanen, saboda masu garkuwar ba a wuri daya su ke ba, sun kasu ne sansanoni daban-daban.

Ya ce korafin masu garkuwar dai bai wuce cewa ana bin Fulani da wadanda su ka ji da wadanda ba su ji ba, ba su gani ba ana kashewa.

Daga nan sai ya shawarci gwamnatin tarayya ta yi masu afuwar gyaran hali.

Ita kuwa Gwamnatin Jihar Neja, ta yi roko ga ‘yan bindigar da ke cikin dazukan su ajiye makamai su rungumi zaman sulhu domin wanzar da zaman lafiya a fadin jihar.

Sakataren Gwamnatin Jihar Neja Ahmed Matane, ya roki ‘yan bindiga su ajiye makamai a yi sulhu.

A jawabin da ya yi wa wani gungun ‘yan bindiga, inda su ka je zaman sulhu da Gumi, a Dutsen Magahi cikin Karamar Hukumar Mariga, Matani ya roki masu garkuwa su ajiye makamai a yi sulhu da su.

Ya roke su su sa hannu domin a sako wadanda aka yi garkuwa da su a ranar Laraba.

Wasu daga cikin kwamandojin mahara sun yi jawaban godiya da kuma nuna amincewar a yi sulhu matsawar gwamnati za ta cika alakwarin da za ta dauka.

Share.

game da Author