Hukumar Hana Sha da Fataucin Muggan Kwayoyi (NDLEA) ta yi gagarimin kamu na kwayar ‘cocaine’, wato hodal Ibilis har ta zunzurutun kudi naira bilyan 32.
An kama kwayoyin a tashar jiragen ruwa ta Tinka Ila (Tincan Island).
An shigo da dilolin kawayoyin ne cikin Najeriya daga Bazin, wadanda sun kai dauri 40, masu nauyin kilogiram 43.11.
An kiyasta kudin su a arashin kan titi zai kai naira bilyan 32.
Kwamandan NDLEA da ke Tashar Ruwa ta Tincan Island, mai suna Sumaila Ethan, ya bayyana wa manema labarai haka a cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Hulda da Jama’a na NDLEA da ke Abuja, Jonah Achema ya fitar.
Ethan ya ce NDLEA na ci gaba da farautar gaggan masu safara da tu’ammali da muggan kwayoyi da masu shigo da kwayar cikin Najeriya.
Ya ce dalilin irin wannan gagarimin aikin da su ke yi babu dare babu rana ne har su ka yi wannan babban kamu na hodar ibilis mai tarin yawa.
Ya ce bayan an sauke kayan, jami’an NDLEA sun dana tarko har tsawon kwanaki da yawa domin su ga masu kayan.
A karshe dia a cewar sa, bayan wasu kwanaki, sai wasu masu fiton kaya, wato ‘ejan ‘yan kiliyarin’, su ka je domin fitar da kayan a ranar 8 Ga Fabrairu, 2021.
“ Nan da nan aka damke su tare da kayan tulin kwayoyin wadanda aka shigo da su ta cikin jirgin ruwa mai lamba MV SPAR SCORPIO. Shi ma jirgin an yi masa binciken kwakwaf.
“Bayan mun kai kwayoyin dakin gwaji, an tabbatar cewa hodar Ibilis ce.”
“ Mun damke ejan din da su ka je yi wa kwayar fito daga cikin tashar jirage ta Tincan Island. Yanzu haka sun a tsare, kuma ana ci gaba da bincike.
Daga nan ya gode wa sabon Shugaban NDLEA Burgediya Janar Buba Marwa, wanda ya rika ba su shawarwarin da har aka yi nasarar damke ejan din kwayar su biyu.
Ya ce an samu wannan nasara ce bayan an samu irin wannan nasarar a wani babban kamu kwayoyi da NDLEA ta yi a Tashar Filin Jiragen Sama na Lagos da Abuja da kuma wani kamen a jihohin Edo, Katsina, Nasarawa da Benuwai.