Gwamnatin Najeriya ta ki amincewa da shawarar da Bankin Bayar da Lamuni na Duniya (IMF) ya bayar cewa wajibi ne kasar ta karya darajar naira domin ceto tattalin arzikin ta.
Najeriya ta bayyana cewa idan ta yi haka, to jama’a a su kara shiga uku sau uku, domin farashin kayan abinci da kayan masarufi da dukkan kananan kayan amfanin gida ga masu karamin karfi zai hauhawa sosai.
IMF dai ta ce karya darajar naira shi ne zai bunkasa karfin tattalin arzikin masu kananan kasuwanci, domin darajar naira a gaban dala da kudaden kasashen waje irin su fam da Yuro, ba ta kai yadda Najeriya ke tinkaho ta kai ba.
IMF na ganin cewa Najeriya ta tsula wa naira daraja da karin kashi 18 cikin 100, shi ya sa tattalin arzikin kasar ke ci gaba da yin dabur-dabur, dawurwura da kara nausawa cikin kunci da tsadar rayuwar da ake ci gaba a fuskanta a cikin kasar.
“Wannan gurguwar shawara ce, IMF na neman dora kasar nan a kan hanyar da idan aka bi, ba mai bullewa ba ce. Sukuwa IMF ke son dora Najeriya a kan makahon doki.” Inji Najeriya, ta na maimaita cewa karya darajar naira zai kara haifar da tsadar kaya a kasar nan.
Cikin shekarar da ta gabata dai Najeriya ta karya darajar naira domin cike gibin da ke tsakanin arashin kudaden kasashen ketare a kasuwanni, wadanda su ka sha bamban da farashin gwamnati da ake bayarwa a bankuna.
Hakan kuwa ya zo ne sanadiyyar kwankwatsar da annobar cutar korona ya yi wa tattalin arzikin Najeriya, inda aka shafe watanni ‘yan kasuwa, masana’antu da cibiyoyin hada-hada da kasuwanni na kulle.
Sannan kuma a lokacin kasuwar danyen mai a duniya ta tsaya cak, ta yadda ko kyauta aka bayar da danyen mai, babu mai bukata. Har ta kai danyen mai bai kai darajar ruwan cikin tulun dan garuwa ba.
Sai dai kuma IMF na ganin har yanzu tsarin sabat-ta-juyat-tar naira da dala a kasar nan da kasashen waje ya hana asusun kasar na waje kara bunkasa, alkadarin sa ba ya da wata muhibba. Haka kuma cikin gida a kullum naira na shan kashi a wajen dala, saboda babu takakaimen farashi, sai irin yadda dala ta ga dama ta ke karkata akalar naira a kasuwa.
A yanzu dai a ma’aunin masu zuba jari da masu hada-hadar kaya daga kasashen waje, naira 398.50 na daidai da dala 1.
Wato kenan a ranar Litinin dala ta tashi daga naira 397.50.
Amma a hannun ’yan canji, su na sayar da dala 1 a kan naira 480.
Shi ya sa IMF ta ce Najeriya ba ta wani takamaimen tsarin da zai iya hana farashin dala dagawa sama, tare da hana naira shan dukan tsiya a hannun dala a kasuwar cikin gida ballantana a kasuwannin kasashen waje.