Hukumar Kula da Harkokin Mai ta Najeriya, wato NNPC, ta bayyana cewa Najeriya ta sayar da fetur da gas na dala bilyan 2.89 daga watan Nuwamba, 2019 zuwa watan Nuwamba, 2020.
Najeriya dai ta samu gagarimar asarar kudaden shiga a cikin shekarar 2020 sakamakon bullar cutar korona.
Cikin rahoton da NNPC ta fitar ta ce an samu rara ta naira bilyan 13.43 cikin watan Nuwamba 2020, ba kamar watan Oktoba 2020 ba, wanda aka samu rarar naira bilyan 8.71 kacal ba.
NNPC ya ce an samu karin kashi 54 na rara kenan tsakanin watannin biyu masu jere da juna.
Daya daga cikin Manyan Manajojin NPPC, mai suna Kennie Obateru ne ya itar da wannan sakamakon rahoto.
Rahoton dai ya na dauke da hada-hadar kasuwancin mai da gas wanda aka yi tsakanin watan Nuwamba na 2019 zuwa watan Nuwamba na 2020.
Ana tantance rara ko gibin hada-hadar cinikin mai ne idan aka cire kudaden wahalhalun da ake yi wa maitun daga hako shi har zuwa lokacin da aka sayar da shi.
Za a cire adadin kudaden hada-hadar daga cikin ribar da aka samu. Abin da ya yi saura, ya zama rara kenan.
Idan kuma adadin kudaden da aka yi wa mai wahalhalu sun zarce yawan ribar da aka samu, to an samu gibi kenan.
Cinikin da aka yi cikin watan Nuwamba, 2020 na naira bilyan 409.65, bai kai na watan Oktoba da aka samu naira bilyan 423.08 ba.
Don haka tsakanin watan Oktoba zuwa Nuwamba na 2020, an samu bambancin karancin ciniki, har na naira bilyan 13.43 kenan.
Yawan danyen mai da aka sayar ya taimaka da samar da dala milyan 73.09, wato kwatankwacin kashi 67.17 na dalolin da aka yi hada-hada, idan aka kwatanta da dala milyan 12.38 kacal da aka yi hada-hada a watan da ya gabata na baya.
Yayin da gas wanda aka fitar da shi waje aka sayar a wancan watan ya kai na dala milyan 35.75 a cikin watan.
Wannan ya nuna cewa jimillar mai da gas wadanda Najeriya ta sayar a kasuwannin waje sun kai na dala bilyan 2.89 daga watan Nuwamba, 2019 zuwa watan Nuwamba, 2020.