Najeriya ta sauya takun ririta kudaden bashin da ta ke ciwowa

0

Najeriya ta kara geji da malejin iyakar bashin da za ta iya riritawa, daga kashi 25% zuwa kashi 40%. Haka dai Hukumar Sa-ido kan Tulin Bashin da ake bin Najeriya (DMO), wato ‘Debt Management Office’ ya bayyana a Abuja.

Majalisar Zartaswa ce ta amince da wannan tattagar masaki kan batun ciwo bashi a taron da ta yi ranar 10 Ga Fabrairu, a Fadar Shugaba Muhammadu Buhari.

Sun amince da sabon tsarin a matsayin mafita ga tsarin ciwo bashi da kuma mafita ga tsarin biyan bashi a tsakanin shekarun 2020 zuwa 2023.

DMO ya ce wannan tsari zai kara bayar da rata ko tazarar lokacin biyan bashi zuwa tsawon shekaru 10, musamman saboda rufa wa kasuwar cikin gida asiri.

Wannan tsarin a cewa Ofishin DMO zai tabbatar da gwamnati ta samu yi wa bashin da ta ke ciwowa rikon-kazar-kuku, domin a samu lokacin da za a rika biyan bashin ba tare da an ji jiki ba.

“Najeriya na da sharuddan yarjejeniyar aiki da kudaden bashi da ka’dojin biya, wato akwai na 2021 zuwa 2015 sai kuma na 2016 2019.”

Haka ofishin ya bayyana a cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Laraba.

“An canja tsarin biyan bashin ne domin yin la’akari da yadda cutar korona ta yi wa tattalin arziki illa a cikin gida da duniya baki daya. Saboda daha sabon tsarin yay i daidai da gaskiyar lamarin halin da tattalin arzikin kasar nan da kuma duniya ke ciki.”

An kiyasta cewa kudin ruwan da za a samu a cikin kudin shiga a 2021, za su ragu zuwa kashi 60.8%, idan aka yi da kashi 92.%.

Sai dai kuma ana jin kudin shigar zai karu zuwa kashi 94% nan da zuwa shekarar 2025.

Masu sharhin tattalin arzikin kasar nan na ganin cewa ya zama wajibi Najeriya ta shiga taitayin ta wajen riritawa da manejin kudaden da ta ke biyan bashi, ta kara himma wajen tara kudaden shiga, sannan kuma a rage tabargaza da almubazzaranci da kudade tare da daina kashe kudaden gwamnati a wuraren da ba su zama dole ba.

Share.

game da Author