Gwamnatin Najeriya ta kasa wa’adin hada lambar waya da lambar Katin Shaidar Dan Kasa (NIN).
Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa za a iya ci gaba da hada lambar waya da lambar katin dan kasa daga nan har zuwa ranar 6 Ga Arilu, 2021.
Wannan karin wa’adi har na makonni takwas ya fito daga bakin Ministan Harkokin Sadarwa Isa Pantami, a lokacin taron kwamitin tilasta hada lambar katin waya da lambar katin dan kasa.
Pantami ya ce wa’adin kwanaki masu yawa da aka kara, zai bai wa kowane dan Najeriya da mazaunin kasar a tsanake domin tabbatar da cewa ya samu dama kusan ta karshe da zai hada katin san a dan kasa da lambar wayar sa.
Minista Pantami ne ya shugabanci taron, wanda ya samu damar halartar Shugaban Hukumar Rijistar Katin Dan Kasa (NIMC), Shugaban Hukumar Inganta Fasahar Zamani (NITDA) da kuma Shugaban Kungiyar Kamanonin Tarho da Sadarwa Masu Lasisi na Kasa (ALTON).
Sauran sun hada da shugabannin MTN, Airtel, 9Mobile, Ntel, Spectranet, SMILE da na Globacom.
Tuni dai har wadannan kamfanonin layukan wayoyi su ka karbi lambobin katin dan kasa har milyan 56.18, domin ci gaba da yin rajistar katin dan kasa ga wadanda har yanzu ba su mallaka ba, ballantana su hada lambar na su katin da lambobin wayoyin su.
Zuwa yanzu dai akwai cibiyoyin yin rajistar katin dan kasa har 1060 a adin kasar nan. Sannan su ma kamfanonin sayar da layin waya sun bude daruruwan cibiyoyin yin rajistar katin dan kasa, domin saukakawa da kuma hanzarta kammala aikin.
Har yanzu dai Minista Pantami na ci gaba da shan suka, ganin yadda ya tattago aikin tilasta wa ‘yan Najeriya hada layukan wayoyin su tare da lambobin katin dan kasa, a daidai lokacin da korona ke kara fantsama a kasar nan, musamman ganin yadda aka rika samun cinkoso, saboda kusan kashi 75 na ‘yan Najeriya bas u mallaki katin dan kasa ba.
Discussion about this post