Shugaban Bankin Bunkasa Kasashen Afrika, wato AfDB, Akinkumi Adesina, ya goyi bayan sake fasalin Najeriya ta yadda kasar za ta rika bunkasa albarkartun tattalin arzikin da ke shimfide a cikin ta.
Adesina ya yi mamaki da takaicin cewa duk da Najeriya na da albarkacin tunkuzar daden kwalta, wato ‘bitumen’ wadda za ta iya kai har ta dala tiriliyan 1.5, sai ga shi kuma kasar nan na kashe makudan kudade har naira bilyan 300 wajen shigo da tunkuzar daben kwalta daga kasasshen waje.
Adesina ya yi wannan furuci ne yayin da ya ke jawabi a matsayin babban bako wajen bikin sake rantsar da Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo, a Akure, babban birnin jihar, a ranar Talata.
Shugaban na ‘African Development Bank, cewa ya yi matsawar Najeriya na so ta fita daga murdadden matsin tattalin arzikin da ta ke ciki har ta ci gaba a duniya, to dolle sai an canja taku da fasalin fedaraliyya, yadda za a tashi haikann a alkinta albarkatun da ke fadin kasar nan, maimakon a bar su a wulakance ana dogara da danyen man fetur kawai.
“Shi fa tsarin Federaliyyar da Najeriya ke a kai, ba ya bunkasa sauran yankunan kasar nan. Shi ya sa kullum tattalin arzikin Najeriya ke tuma tsalle wuri daya ya na zubar da gumi karcat, maimakon a ce gudu ya ke yi zuwa tudun-mun-tsina ya na gumin.”
“Akalla a kasar nan akwai albrkatun bakar tunkuzar daben kwalta shimfide a kasa za ta kai ta dala tiriliyan 1.5, tare da kiyasin ganga bilyan 16 a nan cikin Jihar Ondo.” Inji Adesina.
Ya ce amma abin takaici ne duk da irin albarkacin dankon bakar tunkuzar daben kwalta da ake da shi a Jihar Ondo, titinan jihar ko bakar tunkuzar ba a dabe su da ita ba.
“Wannan abin haushi, takaici da kunya ne, a ce ga mu da dimbin albarkatun dankon tunkuzar daben kwalta, amma duk shekara sai an kashe bilyoyin nairori ana shigo da ita daga kasashen waje.