NAFDAC ta kama gangunan burkutu 22 a jihar Adamawa

0

Kodinatan hukumar NAFDAC reshen jihar Adamawa Jamilu Audu ya bayyana wa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa hukumar ta kama gangunan 22 cike makil da burkutu a jihar.

Audu yace an kama motar da aka loda kayan wadannan ganguna na Burkutu a hanyar Jimeta-Girei da misalin karfe 2 na dare a 2020.

Ya bayyana cewa ko da masu motan suka hango jami’an NAFDAC, sai suka watsi da motar suka arce cikin daji.

” bayan an gudanar ga gwaje-gwaje akai an gano cewa wannan burkutu idan mutum ya sha zai antaya cikin matsala na rashin lafiya domin ba abin sha bane, kamar yadda gwajin ya nuna.

Bayan haka ya ce an kama wasu daga cikin wadanda ke safarar wadannan ganguna na burkutu sannan kuma an kama kwayoyi na jabu da ake sarrafawa a jihar ana saida wa mutane da wasu muggan kwayoyi.

Share.

game da Author