Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum shida sun kamu da sabuwar nau’in cutar korona mai suna ‘B117’ a Najeriya.
Shugaban hukumar Chikwe Ihekweazu ya sanar da haka a taron da kwamitin PTF ta yi da manema labarai ranar Litini.
Ya ce masana kuma likitoci masu bincike a cibiyar ACEGID na jami’ar Redeemers dake jihar Osun ne suka gano cutar a jikin wadannan mutane.
Bisa ga sakamakon gwajin ACEGID an gano mutum biyar yan asalin jihar Osun, daya kuma a jihar Kwara kuma ga dukkan alamu sabuwar nau’in ta fara yaduwa a Najeriya yanzu sosai.
Ihekweazu ya ce NCDC za ta tsananta yin gwajin cutar musamman a jikin matafiyan dake shigowa kasar nan daga kasashen UK da Afrika ta Kudu.
Ya ce hukumar za ta hada hannu da hukumar NIMR domin ci gaba da yin gwajin cutar a jihohin Osun da Kwara.
Ihekweazu ya ce har yanzu ba a tabbatar ko a dalilin barkewar sabuwar nau’in cutar ne ke ake samun karuwa a yaduwar cutar a kasashen UK da Afrika ta Kudu ko kuma rashin kiyaye dokokin guje wa kamuwa da mutane ke kin yi ne kawai.
Sai dai kuma BBC ta rawaito cewa wani babban jami’in gwamnatin UK ya ce sabuwar nau’in cutar ba ta da illa kamar nau’in cutar ta farko amma mutane sun fi saurin kamuwa da ita.
Ya kuma ce maganin rigakafin da ake da shi yanzu na da ingancin kashe sabuwan nau’in cutar.
Sabuwan nau’in cutar Korona ‘B117’
A watan Satumba Kasar Birtaniya ta sanar da bayyanar wata sabuwar samfurin Korona da take mamaye mutanen kasar sannan ana samun karin mutanen kasar da ke ta mutuwa babu kakkautawa da dalilin kamuwa da wannan cuta.
Ita dai wannan nau’in Korona mai suna “lineage B.1.1.7” ta bayyana da tsanani a kasar Birtaniya, yasa dole gwamnatin kasar ta saka sabbin dokoki na dakile yaduwarta da suka hada da dokar shiga da fice da balaguro a fadin kasar.
Sakamako gwajin cutar da ‘Worldometers.com’ ya nuna cewa mutum miliyan hudu sun kama cutar korona inda daga cikin mutum 100,000 sun mutu.
BBC ta rawaito cewa sabuwar nau’in cutar korona ta bullo a kasashen sama da 45 sannan ga dukkan alamu za a samu karuwa a kasashen da cutar za ta bullo a duniya.
Discussion about this post