Mutum 30,000 ke mutuwa duk shekara a dalilin busa taba sigari a Najeriya – Rahoton Bincike

0

Sakamakon binciken da cibiyar binciken tattalin arzikin Afrika (CSEA) ya nuna cewa a duk shekara taba sigari na yin ajalin mutum 28,876 a Najeriya.

Jami’in cibiyar Marco Castradori ya gabatar da wannan sakamako a taron tattauna illolin dake tattare da busa taba sigari da tattalin arzikin kasar nan da aka yi a jihar Kano.

Sakamakon binciken ya kuma kara nuna cewa cutar dake toshe zuciya da ake kamuwa da ita a dalilin busa taba sigari na kashe mutum kashi 29, sauran cututtukan dake kama zuciya na kashe mutum kashi 17.5 sannan ciwon shanyewar bangaren jiki na kashe mutum kashi 13% da sauran su na cikin cututtukan dake kisan masu zukan taba sigari a Najeriya.

A fannin kasafin kudin ƙasa idan Najeriya ta kashe Naira biliyan 634 wajen magunguna Naira biliyan 526.45 daga cikin wannan kudade na tafiya wajen siyan maganin cututtukan da ake kamuwa da su a dalilin zukan taba sigari.

Sannan Naira biliyan 526.45 da aka kashe ya kwashi kashi 0.32% na kudaden da kasan ta samu a shekaran 2019 sannan da kashi 9.63% na kudaden da fannin kiwon lafiya ke kashewa a shekara.
Castradori ya ce Najeriya za ta iya kauce wa asaran da taban sigari ke kawowa idan ta kara kashi 50% na farashin sigari a kasan.

Ya ce yin haka zai taimaka wajen samun karuwa a kudaden haraji da kasan za ta samu sannan da ceto rayuwar mutane 23,838 daga mutuwa a dalilin zukan taba na tsawon shekara 10.

A cikin wannan Faburairu PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta fara amfani da dokokin hana siyar da taba sigari a kasar nan.

Kungiyoyi wanda a ciki akwai ‘Nigeria Tobacco Control Alliance (NTCA)’ da ‘Environmental Rights Action/Friends of the Earth Nigeria (ERA/FoEN)’ be Suka yi wannan kira.

Kungiyoyin sun ce rashin fara aiki da wadannan dokoki na iya kawo cikas ga kiwon lafiyar mutane a dalilin illolin dake tattare da busa taba

Share.

game da Author