Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC Chikwe Ihekweazu ya bayyana cewa mutum 29 sun kamu da sabuwar nau’in cutar korona mai suna ‘B117’ a Najeriya.
Ihekweazu ya fadi haka ne a taron da kwamitin PTF ta yi da manema labarai ranar Litini a Abuja.
Ya ce an gano wadannan mutane a jihohin Edo, Kwara, Lagos, Osun, Oyo da babban birnin tarayya Abuja.
Ihekweazu ya ce masana kuma likitoci masu bincike a cibiyar ACEGID na jami’ar Redeemers dake jihar Osun ne suka gano cutar a jikin wadannan mutane.
Ya ce ga dukan alamu cutar ta yadu a kasar nan a dalilin haka likitocin za su ci gaba da budanar da bincike domin gano sauran mutanen da suka kamu da cutar.
Idan ba a manta ba PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda wasu mutum 13 suka kamu da cutar a Najeriya.
A lokacin an gano wadannan mutane a jihohin Osun, Kwara da Abuja.
Ihekweazu ya ce hukumar NCDC da likitoci masu bincike a cibiyar ACEGID na jami’ar Redeemers za su tsananta yin gwajin cutar musamman a jikin matafiyan dake shigowa kasar nan daga kasashen UK da Afrika ta Kudu.
Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ce zuwa yanzu cutar ta bullo a kasashe 80 a duniya.
Sannan har yanzu babu samfurin nau’in cutar B.1.351 da ta bullo a kasar Afrika ta Kudu.