Mijina ya darkaki yin tsafe-tsafe don ya mallake ni – Matar wani Magidanci a Kotu

0

Wata mata mai suna Bukola Ejalonibu ta shigar da kara a kotun Mapo dake Ibadan domin kotun ta raba aurenta na shekar 23 a dalilin wai ta gano mijin ta Kokawole na yayyafa mata asiri kafin ya kwana da ita.

Bukola ta ce rayuwarta na cikin mummunar hadari domin baya ga yi mata tsafe-tsafe kafin ya kwanta da ita kasurgumin mashayi.

“A duk lokacin da Kolawole ya yayyafa min asiri suma nake yi.

“Wata rana Kolawole ya watson kayana waje sannan ya lalata duk kayan dake shago na.

Bukola ta ce raba auren shine kadai mafita musamman yadda rashin yin haka ka iya kawo ajalinta.

Kolawole ya musanta abin da Bukola ta fadi a gaban alkali sannan ya kara da cewa Bukola bata da godiyar Allah ne

“Na Bude wa matata babban shago kuma nakan bata kudin kashewa akai-akai amma duk da haka bai ishe ta ba tana shiga tana fita don ta ga baya na kawai don ta mallaki dukiya ta.

Alkalin kotun Ademola Odunade ya raba auren sannan ya raba ‘ya’yan gida biyu, Bukola zata dauki biyu daga ciki sannan shima mijin nata zai dauki biyu tunda ‘ya’yan dama hudu ne.

Odunade ya ce Kolawole zai rika biyan Naira 10,000 domin ciyar da ‘ya’yan sa dake wajen Bukola.

Share.

game da Author