A dalilin sace daruruwan dalibai mata ‘yan makaranta da aka yi a Jangebe, karamar hukumar Talatan Mafara, jihar Zamfara, mazauna garin Jangebe sun gudanar da zanga-zangar nuna gazawar gwamnati na samar musu da tsaro a yankin.
Matasa sun fito titunan garin Jangebe inda suka rika kai wa motocin gwamnati da na ‘yan jarida hari cikin fushi saboda sace dalibai da mahara suka yi.
Matasan sun tattare mashigan garin Jangebe don hana duk wani jami’in gwamnati shiga gari,
Duk wanda ya tunkaro sai ya ji ruwan duwatsu ta ko-ina. A haka dai har wasu sun samu rauni, wasu motoci kuma sun fada tarkon matasan.
Har zuwa wannan lokaci da muke kawo muku rahoto, ana zaman tashin hankali da dar-dar a Jangebe, inda mutanen gare suke cike da rashin natsuwa da tashin hankali.
Gwamna Matawalle ya bayyana cewa tuni gwamnati ta aika da jami’an tsaro domin a ceto wadannan yaran makaranta.
“Za mu rika sanar da iyayen daliban halin da ake ciki.
Matawalle ya yi kira ga mutanen jihar gaba daya da su hada hannu da gwamnati da bata goyon baya don ganin an yi nasaran ceto daliban daga hannu mahara.
“Ina kira ga mutane da kada su yadda a hure musu kunne da shigo da siyasa cikin al’amarin da ya faru domin yin haka ba zai haifar musu da da mai Ido ba.