Mata ta kan gaggaura min mari idan na hukunta ‘ya’yanmu – Magidanci a Kotu

0

Wani magidanci ya bayyana wa Kotu cewa matarsa mai suna Iyabo, kan daddalla masa mari duk lokacin da ya hukunta ya’yan sa.

Magidancin i mai suna Oyeniyi Oyedepo ya roki Kotu ta raba auren sa da matarsa Iyabo saboda rashin kunya, fitsara da sharara masa mari da take yi.

” Wai shi kenan ace mutum bashi da iko akan ya’yan sa, babu damar su yi laifi ni kuma in yi musu hukunci a matsayina na mahaifin su sai ta dira a kaina ta rika sharara min mari.”

Iyabo ta amsa laifinta a gaban Alkali, sai dai ta ce ba haka kawai take gaura wa mijin mari ba,” Mijia kazamin gaske ne kuma, baya tsaftace kansa sannan yana kiwo a gida, sam sam baya kula da su. A dalilin haka ne dan ya naga haka sai in gaggaura masa mari domin ya dawo hayacin sa.

Iyabo wanda yar kasuwa ci ta bayyana wa kotu cewa ita ma fa auren ya gundireta hakanan, alkali ya raba su kawai.

Sai dai kuma alkalin Kotun ya ce ba zai raba auren ba saboda akwai yiwuwar za su iya sasantawa.

Ya umarci yan uwan Iyabo da na Oyedepo su shiga lamarin domi kawo karshen rashin jituwar da ke tsakanin ma’auratan.

Share.

game da Author