Zuwa ranar Laraba bayan rufe kofar Kasuwar Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari ta Najeriya (NSE), manyan kamfanoni da gaggan masu hannayen jari sun sake dibga asarar naira bilyan 426.
Hakan ya nuna cewa a cikin watan Fabrairu sun dibga asarar naira tiriliyan 1.
Masu zuba jari dai sun zabga hannayen jari masu yawa a Fidson, CAP, Regal Insurance, STI da kuma Sunu Assurance domin sayarwa. Wannan ya haifar sa tangal-talgal din jirgin fiton hada-hadar baki daya.
Kasuwa ta yi wa masu zuba jari gwatson-kyanwa, saboda kamfanoni 37 sun dibga asara, yayin da 13 kadai su ka yi abin da Bahaushe ke kira da kyar na tsere ya fi da kyar aka kama ni.
A karshen tashi hada-hadar ranar Laraba dai karfin hannayen jarin kamfanonin ya koma naira tiriliyan 21.290.
Wadanda Kasuwa Ta Fi Yi Wa Duka:
Kamfanin Etranzact ya sha duka har ya yi asarar kashi 10%. Haka CAP shi ma ya y i asarar kashi. Sai Fidson shi ma ya yi kasa da kashi 10%, kamar yadda Sunu Assurance 10% da Sovereign Trust Insurance su ma su ka yi kasa da kashi 10%.
PREMIUM TIMES HAUSA ta kawo yadda a ranar Talata masu zuba jari su ka yi asarar naira bilyan 28 a Kasuwar Hada-hadar Hannayen Jari (NSE).
Masu masu hannayen jari a Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari ta Najeriya sun dibga asarar naira bilyan 28 a zaman hada-hadar ‘kasuwa-ci-mai-tsoron-ki’ da aka yi a ranar Talata.
Hakan ya haifar da asarar naira bilyan 28 a cibiyar hada-hadar ta NSE.
Wannan ya nuna tun da aka shigo sabuwar shekara, masu hannayen jari na ci gaba da shan duka a hada-hadar NSE.
Wadanda su ka fi jin jiki sun hada da NNFM, NEM, Niger Insurance, Japaul Gold da Multiverse, su ke su ka fi samun raguwar hannayen jari da dama.
Amma kuma hakan bai hana samun kamfanoni 23 da su ka yi abin nan da ake cewa mafarauci tsira da na bakin ka ba.
Gurguzun hannayen jarin dungurugun ya ragu zuwa 41,510.23, yayin da adadin kudaden da ke shige-da-fice a hannun masu hada-hadar kasuwanci ya ragu zuwa naira tiriliyan 21.716.
Kenan karkaf daga shekarar nan har zuwa yau, jadawalin raguwar hada-hadar sai kasa ya ke kara yi, har ya kai da kashi 3.08.
Kamfanonin Da Su Ka Ci Riba Sun Hada Da:
Champion Breweries kashi 10%. Morison kuma ya karu da kashi 10% shi ma, kamar yadda RT Briscoe ya karu zuwa 10%. Linkage Assurance shi ma kashi 10% to end today’s trade at N0.66. Wema ya karke a cikinmanya guda 5 da su ka tsira da shan dukan kasuwa da kashi 7.69%.
Manyan Kamfanoni 5 Da Kasuwa Ta Lakada Wa Duka:
NNFM ya yi asarar kashi 9.94%, inda darajar hannayen jarin kamfanin ya tsaya kan N7.79. NEM ya yi kasa da 9.20%, wato darajar hannun jari ta tsaya a naira N2.27. Hannayen jarin Niger Insurance sun samu karyewar daraja zuwa N0.20, inda ya yi asarar kashi 9.09%. Shi ma Japaul Gold ya rankwafa kasa da N0.72, inda ya rasa kashi 8.8%. Multiverse ya cakire a N0.24, kenan hannayen jarin sun yi rashin 7.69%.
PREMIUM TIMES za ta rika kawo rahoton yadda kasuwar hada-hadar hannayen jarin Najeriya ke yin tsallen-badake, domin masu karatu su rika sanin halin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki.