Masu masu hannayen jari a Cibiyar Hada-hadar Hannayen Jari ta Nijeriya sun dibga asarar naira bilyan 28 a zaman hada-hadar ‘kasuwa-ci-mai-tsoron-ki’ da aka yi a ranar Talata.
Hakan ya haifar da asarar naira bilyan 28 a cibiyar hada-hadar ta NSE.
Wannan ya nuna tun da aka shigo sabuwar shekara, masu hannayen jari na ci gaba da shan duka a hada-hadar NSE.
Wadanda su ka fi jin jiki sun hada da NNFM, NEM, Niger Insurance, Japaul Gold da Multiverse, su ke su ka fi samun raguwar hannayen jari da dama.
Amma kuma hakan bai hana samun kamfanoni 23 da su ka yi abin nan da ake cewa mafarauci tsira da na bakin ka ba.
Gurguzun hannayen jarin dungurugun ya ragu zuwa 41,510.23, yayin da adadin kudaden da ke shige-da-fice a hannun masu hada-hadar kasuwanci ya ragu zuwa naira tiriliyan 21.716.
Kenan karkaf daga shekarar nan har zuwa yau, jadawalin raguwar hada-hadar sai kasa ya ke kara yi, har ya kai da kashi 3.08.
Kamfanonin Da Su Ka Ci Riba Sun Hada Da:
Champion Breweries kashi 10%. Morison kuma ya karu da kashi 10% shi ma, kamar yadda RT Briscoe ya karu zuwa 10%. Linkage Assurance shi ma kashi 10% to end today’s trade at N0.66. Wema ya karke a cikinmanya guda 5 da su ka tsira da shan dukan kasuwa da kashi 7.69%.
Manyan Kamfanoni 5 Da Kasuwa Ta Lakada Wa Duka:
NNFM ya yi asarar kashi 9.94%, inda darajar hannayen jarin kamfanin ya tsaya kan N7.79. NEM ya yi kasa da 9.20%, wato darajar hannun jari ta tsaya a naira N2.27. Hannayen jarin Niger Insurance sun samu karyewar daraja zuwa N0.20, inda ya yi asarar kashi 9.09%. Shi ma Japaul Gold ya rankwafa kasa da N0.72, inda ya rasa kashi 8.8%. Multiverse ya cakire a N0.24, kenan hannayen jarin sun yi rashin 7.69%.