Masana diflomasiyya sun roki kada kasar da ta karbi su Buratai a matsayin jakadu

0

Wasu masana huldar diflomasiyya da su ka hada da kwararrun sanin dangantakar kasa da kasa, lauyoyi da malaman koyar da huldar kasashen duniya, sun yi kira ga kasashen duniya kada wacce ta karbi tsoffin hafsoshin tsaron Najeriya, wato su Buratai a matsayin jakadun Najeriya a kasashen su.

Haka kuma cikin wadanda su ka yi wannan kiran har da tsoin jakadun da su ka taba yin aiki a wasu kasashe, su ma sun shiga cikin sahun masu yin wannan kiraye kiraye ga kasashen da Majalisar Dattawa, cewa kada a karbi jakadancin su Buratai a matsayin jakadun Najeriya.

Wasu kuma da ba su gama sanin takamaimen dalilin nadin su ba, su na ganin cewa akwai dai wani boyayyen dalilin da ya sa Buhari ya rufe ido ya kekasa kasa lallai sai ya nada su jakadu, duk kuma da cewa ana ta korafe-korafe a kan hakan.

Wasu da su ka yi wadannan kiraye-kirayen, sun hada da Farfesa Akinjide Osuntokun, wanda tsohon jakadan kasar Jamus ne, kuma malamin tarihi. Sai tsohon daraktan Cibiyar Nazarin Huldar Diflomasiyya (NIIA), wato Bola Akinterinwa, sai babban lauya Tayo Oyetibo da kuma Farfesan Tarihi na Jami’ar Lagos, David Aworawo.

Da yawan su na ganin cewa bai kamata a tura su ba, saboda guntun kashin da ake zargin ke a gindin su.

Wasu masanan cewa su ka yi sun sani duk wata kasar Turai ta yamma da ta san abin da ta ke yi, kamar Birtaniya, Jamus da Amurka da irin su Kanada, ba za su karbe su ba.

Su na ganin kasashen irin su Rasha da Chana ne kadai a su iya karbar su Buratai a matsayin jakadun Najeriya a can kasashen.

Cikin makon da ya gabata PREMIUM TIMES AHAUSA ta buga labarin cewa wasu lauyoyi na ganin Buhari ya nada su Buratai jakadu ne don kange su daga binciken Kotun Duniya.

Wasu lauyoyi sun bayyana kwararan dalilai biyar da su ka su ne dalilin da ya sa Shugaba Muhamadu Buhari ya yi gaggawar nada Tsoffin Manyan Hafsoshin Tsaron Najeriya ya nada su jakadu na kasashe baban-daban.

Lauyoyin sun ce an nada su Laftanar Janar Tukur Buratai mukaman jakadu ne don kada Kotun Kasa-da-kasa ta Duniya (ICC), ta damke su ta tuhume su da laifukan cin zarafin jama’a da kashe-kashen fararen hula.

Yarjejeniyar Diflomasiyyar Duniya ta 29 ta Taron Vienna Convention dai ta kange tare da haramta kamawa ko tuhumar duk wani jakadan wata kasa a tsakanin kasashen duniya, da nufin tuhumar sa da laifin cin zarafin fararen hula.

Wannan ya sa mutane da dama na ganin cewa Buhari ya yi gaggawar nada su Buratai mukamin jakadun ne don kada a tuhumi zargin kashe-kashen da su ka yi kan talakawa a karkashin mulkin sa.

Dama kuma tun a ranar da su ka sauka jama’a ke ta kiraye-kirayen a gurfanar da su a kotun hukunta laifukan cin zarafin jama’a ta duniya.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Tsoffin Hafsoshin Tsaron Najeriya gata, ya nada su jakadun kasashe daban-daban, mako daya bayan ritayar su.

Wannan gaggawar nadi ta jefa zargi a zukatan jama’a da dama, musamman lauyoyi da a yanzu ke cewa an nada su don a kare su daga tuhumar kotun binciken cin zarafin fararen hula.

Wasu zarge-zargen da ake yi masu, musamman Tukur Buratai, ya hada da kisan-kiyashin ‘yan Shi’a da aka yi a Zariya, cikin watan Disamba, 2015, kisan ‘yan kungiyar IPOB da kuma kisan masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki, Lagos, cikin 2020.

Gabriel Olonisakin; Tukur Buratai; Ibok Ibas da Abubakar Sadique ne aka nada mukaman jakadun bayan ritayar su.

PDP Ta Nemi ICC da INTERPOL Su Damke Su Buratai A Hukunta Su:

Dama kuma jim kadan bayan ritayar su, jam’iyyar PDP ta yi kira ga Kotun Duniya (ICC) da INTERPOL su gaggauta kama su Buratai su hukunta.

Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na PDP, Kola Olagbondiyan ya fitar, ya bayyana cewa su Buratai sun aikata kisan rashin imani da kisan kiyashi a kan araren hula.

Mun Samu Bayanan Da Za Mu Iya Bincikar Buratai –ICC

Cikin shekarar da ta gabata ne Babban Mai Gabatar da Kara na Kotun ICC, Fatou Bensouda, ya yi bayanin cewa sun samu gamsassun bayanan da za su iya bincikar su Buratai kan zargin aikata laifuka a yakin ta’addanci da Boko Haram da Sojojin Najeriya ke kan yi.

Sai dai tun a lokacin Buratai ya ce duk surutai ne, amma lamarin ba ya tsorata shi ko firgita shi.

Sulken Kariyar Bincike Da Buhari Ya Lullube Su Burutai:

Yarjejeniyar Vienna Convention Sashe na 29:

“Duk wani jakadan wata kasa ya haramta wata kasa ta kama shi domin bincike ko gurfanarwa kotu, duk irin laifin da ya aikata. Sulken kariya gare su, ba za a kama su ko hukunta su ba.

“Kada kasar da su ke a zaune ta tura jami’ai a binciki gidajen su ko kwace wasu kadarori ko kayayyakin su.

Afam Osigwe da Inibehe Effiong da wasu lauyoyi da dama, sun cika da mamakin wannan gagarimin laifi da Gwamnatin Buhari ke kokarin binnewa.

Sun yi kira kada Majalisar Dattawa ta amince da nadin mukaman jakadun da Buhari ya nada su Buratai.

Share.

game da Author