Martabar Najeriya sai karuwa ta ke yi a idon duniya – Inji Minista Malami

0

Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya bayyana cewa saboda gagarimin ci gaba a bangaren yaki da cin hanci da rashawar da Najeriya ta sa a gaba, martabar kasar sai karuwa ta ke yi a duniya.

Malami ya yi wannan jawabi yayin da ya ke ganawa da jami’an Cibiyar Jaddada Sa-ido kan Nagartar Aiki bisa Ka’ida, a ofishin sa.

“Najeriya ta samu gagarimar nasarar shimfida tsari da akidar yaki da cin hanci da rashawa”, inji Malami.

Yayin da wasu kasashe da dama ke ta hakilon yadda za su kwato dimbin dukiyoyin su da manyan ‘yan siyasar su su ka handame, ita kuma Najeriya ta samu gagarimar nasarar kwato makudan kudade da dimbin kadarori daga wadannan ‘yan siyasa.

Malami ya ce a akin yaki da cin hanci d rashawa da kuma kwato kudade da kadarori daga mahandaman ‘yan siyasa, komai a fili ake yi, ba tare da wata kumniya-kumbiya ba.

Sai dai kuma wannan cika-baki da bugun kirji da Minista Malami ke yi, ya hakan ne bayan da Kungiyar TI ta dora Najeriya a sikelin kasashen da malejin lalacewar cin hanci da rashawa ya kara yi wa katutu a shekarar 2020.

Kungiyar ta ce lalacewar lamarin a shekarar 2020 har ya fi shekarar 2019 muni matuka.

Yayin da kungiyar da ta kai wa Malami ziyara ta bukaci ya gaggauta goya wa majalisa baya a zartas da gyaran dokokin cin hanci da rashawa, Malami ya ce komai dan a hankali ne, a sannu ba da garaje ba.

Malami ya samu kan sa cikin halin zargin hana ruwa gudu wajen tabbatar da hana ruwa gudun gudanar da wasu shari’u da kuma yi wa shirin gurfanar da wasu kafar ungulu.

Shi da tsohon shugaban riko na EFCC, Ibrahim Magu sun zargi juna wajen yi wa shirin EFCC na yaki da rashawa tarnaki da dabaibayi.

Share.

game da Author