Majalisar Dattawa ta amince a sayo wa ‘yan sandan Najeriya barkonon tsohuwa na naira bilyan 1.3, daga cikin naira bilyan 11.3 da ta amince Hukumar Kula da Aikin Dan Sanda ta Kasa za ta kashe a kasafin 2020.
Yayin da za a kashe naira bilyan 1,362,814,243 wajen sayen barkonon-tsohuwa, za a kashe zunzurutun naira bilyan 11 wajen sayen makamai da sauran kayayyakin da jami’an ‘yan sanda ke bukata wajen gudanar da aikin su.
An amince da kashe kudaden bayan Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa mai kula da Harkokin ‘Yan Sanda, Sanata Haliru Jika ya damka wa majalisa rahoton sa.
Wannan kasafi ne tun na 2020, wanda zai kare a ranar 30 Ga Afrilu, 2021.
Daga cikin naira billyan 11.3 da za a kashe wa aikin ‘yan sanda, ga yadda kashe kudaden za su kasance:
1 – Za a sayi motocin sintiri na naira – N7,600,000,000
2 – Makamai da albarusai na naira – N1,000,000,000
3 – Rigar sulken hana albarusai shiga jiki da kuma hular kwano na naira – N469,338,550
Barkonon-tsohuwa na naira – N1,362,814,243
4 – Kayan hana kamuwa da cutar korona na naira – N358,379,191
5 – Magunguna da akayan agajin-gaggawa na naira – N533,894,117
6 – Tebura da kujeru na ofis-ofis na naira – N29,031,000.