Maganin rigakafin Pfizer-BioNTech na samar da kariya sama da kashi 70% daga cutar Korona – Bincike

0

Sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa allurar maganin rigakafin cutar korona na ‘Pfizer-BioNTech’ guda daya tal na Samar da kariyar kashi 70% daga cutar korona sannan allurar rigakafin guda biyu na samar wa mutum kariyar kashi 80% daga cutar.

Sakamakon binciken ya nuna cewa maganin rigakafin ‘Pfizer-BioNTech’ na samar da kariya daga kamuwa da cutar sabuwar nau’in Korona B.1.1.7.

Ma’aikatar lafiya ta kasar Ingila PHE ce ta gudanar da wannan bincike a jikin wasu ma’aikatan lafiya masu shekaru 60 zuwa sama a kasan.

Sakamakon binciken ya nuna cewa allurar maganin rigakafin guda daya na samar da kariya kashi 57% wa mutane dake da shekaru 80 zuwa sama.
Hakan na faruwa ne bayan makonni 3 zuwa 4 da yin allurar rigakafin.

Sannan allurar rigakafin guda biyu na samar da kariya kashi 85% a jikin masu shekaru sama da 80.

“Ko da mutum ya kamu da cutar bayan yin allurar rigakafin ba zai galabaita ba ko kuma ya mutu ba.

“Hakan ya nuna cewa a ta dalilin maganin ‘Pfizer-BioNTech’ za a samu ragowar kashi 70% a yawan mutanen da ake killacewa a dalilin kamuwa da cutar sannan da yawan da cutar ke kashewa.

Share.

game da Author