Sakamakon wani bincike da aka gudanar kan sahihanci maganin rigakafin cutar korona na kamfanin Johnson & Johnson ya nuna cewa allurar maganin rigakafin guda daya na samar da kariya har kashi 72% da kashi 64% daga kamuwa da cutar a kasashen Afrika ta Kudu da Amurka.
Hukumar kula da ingancin magani da abincin na kasar Amurka FDA ta gabatar da sakamakon ranar Laraba.
Bayan haka sakamakon binciken ya nuna cewa maganin rigakafin Johnson & Johnson na samar da kariya kashi 86% na kwayoyin nau’in korona dake yaduwa a Amurka sannan da kariya daga kashi kashi 82% na kwayoyin cutar dake yaduwa a kasar Afrika ta Kudu.
Hakan ya nuna cewa a dalilin maganin rigakafin Johnson & Johnson za a samu ragowar yaduwar cutar korona musamman sabuwar nau’in cutar dake yaduwa.
Bisa ga wannan bincike FDA ta ce za ta amince da ingancin maganin rigakafin maganin domin moriyar Amurika da kasashen duniya kuma.
PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin cewa sakamakon wani bincike da aka gudanar ya nuna cewa allurar maganin rigakafin cutar korona na ‘Pfizer-BioNTech’ guda daya tal na Samar da kariyar kashi 70% daga cutar korona sannan allurar rigakafin guda biyu na samar wa mutum kariyar kashi 80% daga cutar.
Ma’aikatar lafiya ta kasar Ingila PHE ce ta gudanar da wannan bincike a jikin wasu ma’aikatan lafiya masu shekaru 60 zuwa sama a kasan.
Sakamakon binciken ya nuna cewa allurar maganin rigakafin guda daya na samar da kariya kashi 57% wa mutane dake da shekaru 80 zuwa sama.
Hakan na faruwa ne bayan makonni 3 zuwa 4 da yin allurar rigakafin.
Sannan allurar rigakafin guda biyu na samar da kariya kashi 85% a jikin masu shekaru sama da 80.
“Ko da mutum ya kamu da cutar bayan yin allurar rigakafin ba zai galabaita ba ko kuma ya mutu ba.
“Hakan ya nuna cewa a ta dalilin maganin ‘Pfizer-BioNTech’ za a samu ragowar kashi 70% a yawan mutanen da ake killacewa a dalilin kamuwa da cutar sannan da yawan da cutar ke kashewa.