Kwastan sun damke katan 1,024 na jabun magungunan da buhun shinkafa 1,046 na naira milyan 870

0

Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Shiyyar “C” da ke Jihar Imo, ta bayyana kama magungunan jabu har katan 1,024 da sauran haramtattun kayayyakin da kiyasin kudin su ya kai naira 860.

Kwanturola Yusuf Lawal ya shaida wa manema labarai a ranar Laraba cewa an damke wadannan kayan magunguna na jabu tsakanin 1 zuwa 31 Ga Janairun wannan shekara.

Ya yi wannan taron manema labarai ne a ranar Laraba, a Owerri, babban birnin Jihar Imo.

Ya kara da yin bayanin irin kayayyakin da aka damke, wadanda ya ce sun hada har da bugu 1,046 na shinkafar waje, wadda kudin ta ya kai naira milyan 31,380,000.

Akwai kuma tulin sabulun Eva na waje har katan 290, akalla na naira milyan 4,176,000 da wata mota kirar Toyota Corolla, samfurin 2018, wadda ya ce kudin ta zai kai naira milyan 7,354,345.

Lawal ya ce kayan magungunan an shigo da su ne daga kasar Indiya, ba tare da lambar sahihancin maganin ta hukumar NAFDAC ba.

Babban jami’in kwastan din ya kara da cewa duk kayayyakin da aka damke din doka ta haramta shigo da su cikin kasar nan.

Batun shinkafa kuwa cewa ya yi a cikin wani sito ne aka balle aka kwaso ta, bayan an shigo da ita a asirce.

Sannan dukkan gagungunan da aka kama din an damka su a hannun Hukumar NAFDAC, mai sa-ido a kan hana sha, tu’ammali da safarar miyagun kwayoyi.

Share.

game da Author