KWALLON KAFA: Adamawa United ta karya ƙofin rashin cin wasa bayan wasanni 15

0

Rarrafe baya hana isa, sai dai a daɗe ba a kai ba. Kungiyar kwallon kafa ta Adamawa United ta karya ƙofin rashin cin wasa bayan ta yi nasara a wasan ta da Lobi Stars ranar Alhamis.

Stanley Nnanna ya makala kwallo ɗaya mai ban haushi a ragar Lobi Stars bayan Sadiq Lawal ya jefa masa kwallo cikin sauki dab da mai tsaron bayan Lobi Stars.

Adamawa United ce je kasar tebur din gasar Premier League.

Baya ga rashin kuɗi da take fama da shi, ma kon jiya ƴan bindiga suka tare motar ƴan wasan, suka yi musu fashi sannan suka waske da direban motar.

Ranar Laraba aka sako direban a Jihar Anambra bayan an biya ƴan bindigan naira miliyan 1 kudin fansa.

Wannan nasara da Adamawa United ta yi ya faranta wa ƴan kwallon rai fanin cewa kungiyar ce bata taba cin wasa ko da ɗaya ne a wannan kaka ba, gashi yanzu an buga wasanni 15 kenan.

Share.

game da Author