Tun ba a kai ga shekaru biyu bayan da APC ta kori jam’iyyar PDP a Jihar Kwara, inda gaggan ‘yan jam’iyyar APC irin su Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed su ka kori kaka-gidan siyasar tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki, tuni gayyar APC a Jihar Kwara ta watse gida biyu, inda bangaren Lai Mohammed ya koma ’ya’yan Bora a hannun Gwamna Abdulrazak.
Wannan rashin jituwa ta kara fitowa fili a yayin wannan sabunta rajistar APC, wanda Ministan Yada Labarai ya yi kira da a soke aikin sabunta rajistar da APC ta yi a jihar Kwara, wanda Lai y ace ba a gudanar bisa tsarin da dokar jam’iyya ta gindaya ba.
A wani taron manema labarai da Lai Mohammed ya gudanar a ranar Litinin, ya bayyana yadda bangaren Gwamnan Kwara ya handame komai, aka bangaren magoya bayan Lai, ko kuma abin da ya kira bangaren wadanda su ka sha wahalar kafa gwamnati babu komai, amma gwamnan ya handame komai.
Musamman Lai ya nuna damuwa da yadda kwamitin sabunta rajistar ya karya dokokin jam’iyya wajen rabon sabon katin mamba na jam’iyyar APC da za a sabunta rajistar jam’iyyar da shi.
“An haramta wa jami’an da ba aikin su ba ne taba katin sabunta rajista da rike kundin tattara bayanai da sunayen mambobin da su ka yi rajista. Amma duk an kauce wa wadannan dokoki da sharudda, an karya su a jihar Kwara.
“Don haka ina kira da gaggawa a soke sabunta rajistar APC da aka yi a jihar Kwara tare da sake sabuntawa baki daya. Tare da yin adalci da bin ka’idar da dokar jam’iyya ta shimfida.” Inji Lai.
Lai ya zargi kwamitin sabunta rajista da yin bangaranci, da goyon bayan bangaren Gwamna AbdulRazaq.
PREMUM TIMES ta buga abarin yadda aka samu mummunan sabani tsakanin bangaren Gwamna AbdulRazaq da kuma bangaren Lai Mohammed.
Lamarin ya kara muni kwanan nan, inda aka tsige shugaban jam’iyyar APC na Jihar Kwara, Bashir Bolarinwa, wanda ke goyon bayan Lai, aka maye gurbin sa da Abdullahi Samari.
Duk da dai uwar jam’iyya ta kasa da kuma rashen shiyyar Arewa ta Tsakiya sun sa baki, har yau bangarorin biyu ba su maida wukaken su a cikin kube ba.
Discussion about this post