KUƊIN SHIGA: Najeriya za ta sayar da manyan titinan kasar nan ga manyan ‘yan kasuwa

0

Ministan Ayyuka da Gidaje, Babatunde Fashola, ya bayyana cewa Najeriya ta shirya tsaf domin sayar da manyan titinan Najeriya a hannun manyan kamfanoni, a karkashin wani tsari mai suna HDMI.

Fashola ya ce tsarin HMDI zai kara samar da masu zuba jari a manyan titina, wadanda za su rika zuba kudaden su su na gina titina da kuma kula da su.

Ya ce an kirkoro wannan tsarin a karkashin PIDF, NSIA da kuma SUKUK tun cikin 2018, a karkashin shirin yadda za a rika samun kudaden shiga a kan manyan titina, wadanda da wadannan kudaden ne za a rika kula da titinan da kuma gyaran su.

Fashola ya yi wannan jawabi a lokacin da ya ke bayar da katin shaidar bin ka’ida ga ICRC, ya ce tsarin HDMI zai kara ingancin manyan titinan kasar nan, kula da gyaran su, kuma zai samar da sararin jin dadin tafiya a kan manayan titina laifiyayyu ga masu motoci da masu safara da sauran tafiye-tafiye.

Fashola ya ce idan aka fara tsarin, harkokin sufurin motocin haya zai karu, kuma zai kara daraja da inganci sosoi a kasar nan.

Da ya koma kan muhimmancin tsarin ga tattalin arzikin kasa, Fashola ya kara da cewa: “Baya ga bunkasa ayyukan raya kasa da habbaka kadarori, tsarin zai samar da dimbin ayyukan yi ga mutane dubbai a kasar nan, kuma zain kara wa titinan kasar nan zama wasu kafafen samar da tattalin arziki a kasar nan kakaf fadin ta.

“Masu yin tallace-tallace a sambodin allunan kan titi za su samu kudi, kanikawan da za su rika bude garejin gyaran motoci a gefen titina za su samu kudi, haka su ma masu kamfanonin motocin janwe, masu jan motocin da su ka lalace, su ma za su samu kudi.

“Za a samar da wuraren hutawa a kan manyan titina, wuraren shingayen jami’an tsaro, asibitin duba-laiyar wadanda su ka yi hatsari da sauran abubuwan saukake rayuwar matafiya.”

Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje, Babangida Hussaini, ya ce damka manyan titinan ga hannun kamfanoni da ‘yan kasuwa ya zama dole, saboda matsalar rashin isassun kudaden shiga da gwamnatin tarayya ke fama da su, da kuma sauran matsalolin da ke dabaibaye da tsarin aikin gwamnati.

Share.

game da Author