Kotu a Abuja ta umarci mahukunta su bude kasuwannin Wuse, UTC da MURG wanda aka ryfe su ranar Talata saboda karya dokokin korona da kasuwannin suka yi.
Bayan haka kotu ta umarci kowacce kasuwa ta biya taran naira 50,000.
Idan ba a manta ba mahukunta a babban birnin tarayya Abuja sun garkame shahararren kasuwar Wuse dake tsakiyar gari garin Abuja sabo take dokokin korona da mutane ke yi a kasuwar.
Baya ga kasuwar Wuse, gwamnati ta garkame katafaren kasuwra UTC dake Garki da MURG.
Babban dalilin da ya sa gwamnati ta garkame wadannan kasuwanni biyu kuwa shine saboda karya dokokin Korona da mutane ke yi.
Ƴan kasuwa da dama sun shaida wa wakilin mu cewa wannan hukunci da mahukunta a babban birnin tarayyar suka dauka yayi matukar tsauri. Ƴan kasuwan sun yi cincirindo a kofar shiga kasuwannin sun yi tagumi cikin damuwa.
Wani jami’in hukumar FCTA ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa wannan hukunci da hukumar ta dauka ya zama dole kuma shine kawai mafita a gareta domin mutane suna yi wa dokokin kare kai daga kamuwa da Korona kunnen uwar shegu.
Daga yanzu dole masu kula da kasuwanni su tabbatar an kiyaye dokar Korona a duk lokacin da mai siya ko mai siyarwa zai shiga kasuwannin/