KORONA: Za a yi wa ƴan Najeriya miliyan 109 allurar rigakafin cutar – In ji Shu’aib

0

A taron da kwamitin PTF ta yi da manema labarai ranar Litini a garin Abuja shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA Faisal Shu’aib ya bayyana cewa za a yi wa mutum miliyan 109 allurar rigakafin cutar korona daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.

Ya ce gwamnati na sa ran karban kwalaben maganin rigakafin miliyan 57 daga AVATT da COVAX da kuma wasu miliyan 1.5 da 100,000 wanda kamfanin MTN da kasar India suka baiwa Najeriya gudunmawa wanda za a yi amfani da su wajen yi wa wadanda suka dara shekaru 18 allurar rigakafin a kasar nan.

“Mata masu ciki, ma’aikatan kiwon lafiya, jami’an tsaro, tsofaffi da marasa lafiya ne za a yi wa rigakafin cutar da farko.

Share.

game da Author