Sakamakon gwajin cutar da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta fitar na wannan mako ya nuna cewa mutum 4,350 suka kamu da cutar sannan mutum 58 suka mutu a sanadiyyar cutar daga ranar litinin zuwa Juma’a, 19 ga Faburairu.
An yi wa mutum 1,441,013 gwajin cutar a kasar nan. Daga ciki mutum 150,908 sun kamu.
Zuwa yanzu mutum 21,571 na killace a wuraren da aka kula da waɗanda suka kamu sannan kuma an sallami mutum 127,524. Mutum 1,813 sun mutu.
Jihar Legas, Abuja, Filato, Kaduna, Oyo, Rivers, Kano Anambra ne suka fi yawan wadanda suka kamu da cutar a kasar nan.
Tunda aka shiga shekarar 2021 Korona ta tsananta a Najeriya fiye da shekarar 2020 a lokacin da cutar ta bullo a duniya.
Haka kuma mutuwa daga cutar ya karu matuka inda a jere a kwanakin nan sai an samu wadanda suka rasu a dalilin kamuwa da cutar.
Najeriya za ta karbi rigakafin Korona miliyan 16 ‘AstraZeneca’ a cikin Fabrairu.
Shugaban hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko na ƙasa NPHCDA Faisal Shu’aib ya ce Najeriya za ta karbi maganin ‘AstraZeneca’ saboda karancin maganin kamfanin Pfizer da ake fama dashi yanzu a fadin duniya.
Bayan haka Shu’aib ya bayyana cewa za a yi wa mutum miliyan 109 allurar rigakafin cutar korona daga nan zuwa shekaru biyu masu zuwa.
Discussion about this post