Korona ta kashe sama da mutum 500,000 cikin shekara daya a Amurka

0

Sama da mutum 500,000 aka tabbatar da mutuwar su a Amurka, sanadiyyar kamuwa da cutar korona, tsakanin ranar 6 Ga Fabrairu, 2020 zuwa ranar 22 Ga Fabrairu, 2021.

Wani rahoton musamman da jaridar New York Times da kuma Gidan Radiyon BBC su ka fitar daban-daban a ranar Litinin, ya nuna cewa adadain yawan mutanen da korona ta kashe wa Amurka, ya haura adadin yawan wadanda su ka mutu a Yakin Duniya Na 1 da Yakin Duniya Na 2 da kuma Yakin Vietnam.

Adadin mutanen da korona ta kashe a Amurka, sun haura adadin da wasu masana cututtuka su ka yi kintacen cewa cutar za ta kashe a kasar cikin shekara daya.

Mutuwar mutum 500,000 a Amurka ya nuna can ne cutar korona ta fi kisan jama’a da yawa a duniya.

Wani masanin kiwon lafiyar zamantakewar muhalli, Jeffrey Shaman, ya bayyana cewa adadin kisan da korona ta yi a Amurka abin tsoro ne matuka.

“Amma fa ba za a iya cewa korona ta yi kisan jama’a da dama saboda babu yadda za a yi ba. Maganar gaskiya an samu sakaci tun da farko.” In ji shi.

Wadanda korona ta kashe a Amurka sun kai yawan kashi 20% bisa 100% na yawan wadanda ta kashe a duniya.

A kiyasi, duk cikin mutum 670 Amurkawa, to korona ta kashe mutum daya.

Jimillar adadin dai ya nuna cewa adadain yawan mutanen da korona ta kashe wa Amurka, ya haura adadin yawan wadanda su ka mutu a Yakin Duniya Na 1 da Yakin Duniya Na 2 da kuma Yakin Vietnam.

Share.

game da Author