Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 685 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Lahadi.
Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Lahadi sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum –355, Kaduna-58, Nasarawa-46, Kano-40, Akwa Ibom-33, Katsina-26, Ogun-25, Osun-21, Rivers-16, Edo-15, Oyo-13, Ondo-12, Borno-11, Ekiti-9, Kebbi-3, Filato-2
Yanzu mutum 131,242 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 104,989 sun warke, 1,586 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 25,267 ke dauke da cutar a Najeriya.
Ranar Asabar, mutum 1,883 suka kamu a Najeriya, jihohin Anambra, Rivers, Taraba- , Ogun da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.
Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –49,274, FCT–16,863, Filato –7,894, Kaduna–7,661, Oyo–5,417, Rivers–5,276, Edo–3,794, Ogun–3,381, Kano–2,992, Delta–2,323, Ondo–2,300, Katsina–1,864, Enugu–1,738, Kwara–1,936, Gombe–1,606, Nasarawa–1,810, Ebonyi–1,423, Osun–1,516, Abia–1,220, Bauchi–1,142, Borno-957, Imo–1,116, Sokoto – 748, Benue- 848, Akwa Ibom–878, Bayelsa 669, Niger–688, Adamawa–631, Anambra–893, Ekiti–577, Jigawa 460, Taraba 412, Kebbi 270, Yobe-241, Cross River–195, Zamfara 203, Kogi–5.
Karamin ministan kiwon lafiya Olorunnimbe Mamora ya zayyano wasu dalilai da ya sa Najeriya ke samun karuwa a yawan mutanen dake mutuwa sanadiyyar kamuwa da Korona.
Mamora ya ce hakan na faruwa ne a dalilin rashin gaggauta zuwa asibiti da wadanda suka kamu ba su yi.
Ya ce kamata ya yi a rika gaggawar zuwa asibiti da zaran an ga alamun cutar a jiki ba kawai a zauna a gida ana ‘yan dabaru ba.
Bayan haka Mamora ya ce gwamnati na kokarin ganin ta wadata wuraren da ake kula da wadanda suka kamu da korana na’uran samar da iska domin bunkasa aiyukkan inganta kiwon lafiyar marasa lafiya.
Sai dai wasu kwararrun ma’aikatan lafiya sun ce rashin kiyaye sharuddan guje wa kamuwa da cutar da mutane ke yi musamman a jihohi Legas, Kaduna, Filato da babban birnin tarayya Abuja na cikin dalilan da ya sa cutar ke yawan kisan mutane a kasar nan.
Kwararrun sun yi gargadin cewa yaduwar cutar zai karu fiye da yadda ake tsammani idan mutane suka ci gaba da karya sharuddan.