KORONA: Mutum 6 suka rasu, 1634 suka kamu ranar Talata a Najeriya

0

Hukumar NCDC ta sanar da karin mutum 1634 da suka kamu da cutar Korona a Najeriya ranar Talata sannan kuma mutum 6 suka rasu a dalilin Korona a wannan rana.

Alkaluman da hukumar NCDC ta fitar ranar Talata sun nuna sun nuna cewa jihar Legas ta samu karin mutum – 440, Anambra-160, FCT-158, Rivers-134, Abia-103, Oyo-90, Enugu-81, Osun-73, Gombe-54, Kwara-50, Ogun-32, Filato-32.

Akwa Ibom-31, Ondo-24, Borno-23, Delta-23, Ebonyi-21, Taraba-21, Bayelsa-16, Kaduna-15, Nasarawa-13, Jigawa-12, Bauchi-11, Kano-11, Zamfara-4 da Sokoto-2.

Yanzu mutum 133,552 suka kamu da cutar a Najeriya, mutum 107,551 sun warke, 1,613 sun rasu. Sannan zuwa yanzu mutum 24,388 ke dauke da cutar a Najeriya.

Ranar Litini, mutum 676 suka kamu a Najeriya, jihohin Filato, Rivers, Niger, Kano da Babban birnin Tarayya, Abuja ne suka fi yawan wadanda suka kamu.

Har yanzu dai jihar Legas ne ke da mafi yawan wadanda suka kamu da mutum –49,941, FCT–17,071, Filato –7,982, Kaduna–7,679, Oyo–5,550, Rivers–5,483, Edo–3,802, Ogun–3,440, Kano–3,047, Delta–2,346, Ondo–2,339, Katsina–1,864, Enugu–1,829, Kwara–1,986, Gombe–1,678, Nasarawa–1,830, Ebonyi–1,444, Osun–1,620, Abia–1,323, Bauchi–1,157, Borno-980, Imo–1,116, Sokoto – 750, Benue- 848, Akwa Ibom–909, Bayelsa 685, Niger–757, Adamawa–631, Anambra–1,053, Ekiti–579, Jigawa 472, Taraba 433, Kebbi 270, Yobe-241, Cross River–203, Zamfara 209, Kogi–5.

Kungiyar kiristocin Najeriya CAN ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tsananta tilastwa wa mutane bin dokokin Korona a kasar nan.

” Tilasta wa mutane su bi dokokin korona zai taimaka wajen rage yaduwar cutar. Saboda haka muke kira ga gwamnati ta tsananta tilasta wa mutane bin dokokin don rage yaduwar cutar.

Shugaban kungiyar Samson Ayokunle ya yi kira ga kiristoci da su mara wa gwamnati baya wajen kiyaye dokokin guje wa kamuwa da cutar domin kasar ta samu nasarar dakile yaduwar ta.

Hukumar kula da aiyukkan cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko NPHCDA ce ta shirya wannan taro domin wayar da kan fastoci su cigaba da yin kira ga mabiyansu kan kiyaye bin dokokin kare kai.

Share.

game da Author